Daga dukkan alamu yanzu haka kwamitina sabunta katin rijistar na jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ya ki sabunta wa tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, katin zama dan jam’iyyar a mazabarsa dake cikin karamar hukumar Bakura a jihar ta Zamfara, inda lamarin ke zama wani abu na wala-wala.
Bayar da katin sabunta zama cikakken dan jam’iyyar, wanda aka fara shi a ranar 13 ga Fabrairu, 2021, a jihar ya samu jagorancin Alhaji Karetu Lawal tare da wasu mambobi shida, wadanda hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa ta ba su ikon gudanar da aikin a fadin kananan hukumomi 14 da kuma gundumomi 147 tare da ruumfunan zabe 2,716 a fadin jihar.
Wakilin LEADERSHIP A YAU ya ruwaito cewa, Sanata Yerima ya kasance a garinsa na Bakura, hedikwatar karamar hukumar ta Bakura, tun a ranar Juma’ar da ta gabata, musamman don amsar sabon katin ’yan jam’iyyar ta APC, amma kwamitin sake tantancewar ya yi biris da shi, lamarin da ya sa ya dawo zuwa Gusau, babban birnin jihar, a ranar Lahadi, don jiran martanin kwamitin, amma har zuwa hada wannan rahoto bai ji komai daga wadanda ke kula da aikin sabunta rijistar ba.
Da yake mayar da martani game da hakan, Sanata Yarima ya ce, shi dan APC ne mai kishin kasa, sannan ya kara da cewa, kuma bai taba canza jam’iyyarsa ba tunda ya shiga siyasa a 1999.
Sanata Yarima ya kara jaddadawa cewa, “na tuntubi masu ruwa da tsaki, don gano dalilin da ya sa kwamitin yaki ba ni katin jam’iyyar tare da warware matsalar cikin ruwan sanyi, amma abin ya ci tura.”
A bincike da Wakilin LEADERSHIP A YAU ya yi, ya nuna cewa, matakin bai rasa nasaba da zargin ungulu da kan zabo wajan shiga da yake yi a cikin jihar na kusanta kansa da jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, musamman cikin sha’anin gwamnatin PDP.
Idan za a iya tunawa, Sanata Yarima a ranar Asabar yayin da yake Bakura ya kalubalanci masu adawa da gwamna mai ci, Bello Matawalle na PDP, yana mai cewa, kalubalantar gwamnati Matawalle Maradun din kin yardar da hukuncin Allah ne.
A wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, wani jigo a jam’iyyar APC daga karamar hukumar Bakura, Alhaji Bello Dankande Gamji, ya bayyana cewa, ba za a taba ba wa Yarima katin zama dan jam’iyyar APC ba, saboda rawar da yake takawa a jam’iyyar PDP tun daga shekara 2019 zuwa yau.
Gamji ya ce, “tsohon Gwamna Ahmed Sani tun a shekarar 2019 ya fice daga APC kuma ya kasance yana soyayya da jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Zamfara.”
Gamji ya cigaba da cewa, akwai shaidu da yawa da za su tabbatar da cewa Yarima tun daga lokacin ya fice daga APC, ya ba da misali da zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin Bakura na jiha da aka yi kwanan nan, inda ya ce, “Yarima ya bayar da gudunmawa sosai a kan dan takarar PDP sannan kuma ya yi masa yakin neman zabe a boye.
“Ba za mu yarda a yi wa Yarima rajista a cikin APC ba ko me zai faru kuma za mu bijirewa duk wani matsin lamba daga duk wanda zai yi kokarin yi masa rajista a matsayin dan APC.”
Yarima ya bayyana cewa ya tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki da hukumomi don gano dalilan da suka sa kwamitin ya ki yi masa rajista.
Ya ce, har ma ya yi magana da Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban kwamitin riko na APC, Alhaji Mai Mala Buni, kan batun, yana mai jaddada cewa, “har yanzu zan jira ganin matakin karshe da kwamitin ya dauka a kaina.”
Sanata Ahmed Rufa’i Sani Yerima, wanda aka haifa a ranar 22 ga Yuli, 1960, ya kasance gwamnan jihar na Zamfara daga watan Mayun 1999 zuwa Mayu 2007, kuma ya yi sanata na yankin Zamfara ta Yamma na tsawon shekaru 12, sannan ya kuma rike mukamin Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattiwa Ta Kasa.