Abubakar Abba" />

Sabuwar Annoba: Yadda Aka Sace Yara 9 A Kano Aka Sayar Da Su A Kudu

Cikin wata sanarwa da aka rabawa maneman labarai mai dauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Ahmed Iliyas ta hannun kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta bayyana irin yadda rundunar ta samu gagarumin nasarori wajen yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa.

Sanarwar ta ce, a ranar 12 ga watan Satumban da ya gabata ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wadansu mutane da suka hada da Paule Owne, da wata mai suna Mercy Paul Alias masu shekaru 38 mazaunan unguwar Dakata wadanda ake zargi da satar mutane.

An cafke wadanda ake zargin ne a yayin da suke kokarin tafiya da daya daga cikin yaran da suka sace mai suna Haruna Sagir Bako zuwa garin Onitsha na jihar Anambra.

Sun sace yaron ne a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata a yayin da yake dawowa daga makarantar Islamiyya a unguwar ‘Yankaba.

Tun da farko dai mahaifin yaran mai suna Sagir Muhammad Bako ne ya sanar da ‘yan sanda cewa bai ga ‘ya’yan sa ba, masu shekaru 2 zuwa 6.

Sashen binciken ‘yan sanda na musamman da yaki da mugayen laifuka wato Operation Puff-Adder da hadin gwiwar sashen dake yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa, ya bi diddigi kan wadanda  ake zargin, inda bincike ya gano cewa wadnda ake zargi sun jima suna satar mutane a unguwannin Sauna, Kwanar Jaba, Kawo, Hotoro, ‘Yan kaba da kuma unguwar Dakata.

Binciken bai tsaya nan ba ya fadada har jihar Anambra, domin kuwa a ranar 13 zuwa 17 ga watan Satumban da ya gabata, ‘yan sanda sun yi nasarar tseratar da sauran yaran da aka sace daga Kano a can jihar ta Anambra, bayan da barayin suka siyar dasu, wadanda suka hada da, Umar Faruk Ibrahim mai shekaru 10 wanda aka canja masa suna zuwa Onyedika Ogbodo, Aisha Moh’d Abdullahi ‘yar shekaru 9 wadda aka canja mata suna zuwa Ozioma Ogbodo, Usman Mohammed mai shekaru, Amira Auwal, Husna Salisu, Blessing Ogbodo ‘yar shekaru 10, Chiazozie Ogbodo dan shekaru 11, Chiemerie Ogbodo.

Bugu da kari,  mutanen da ‘yan sanda suka cafke kan satar da kuma sayar da yaran sun hada da:

Emmanuel Igwe dan shekaru 34 wanda ya taimakawa masu satar mutanen sai kuma Ebere Ogbodo da wata mata louisa Daru masu shekaru 45 sune dillalan da suka siya suka kuma siyar da yaran.

Sai wata mata Monica Orachaa mai shekaru 50 da suke siyarwa da yaran idan sun sato.

Exit mobile version