Rabiu Ali Indabawa" />

Sabuwar Girgizar Kasa Ta Halaka Mutane Biyar A Philippine

Akalla Mutane 5 sun mutu sakamakon rugujewar gine-gine 2 sanadiyyar wata kakkarfar girgizar kasa da ta dirar wa wani yanki na Kasar Philippines. Rahotanni sun ce an yi nasarar zaro mutane 3 da ginin ya danne su a kauyen Porac, haka zalika wata tsohuwa da jikanta wadanda su ma wani ginin na daban ya hallaka a Lubao.
Gwamnan yankin Pampanga da ya fuskanci girgizar kasar Lilia Pineda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni jami’an agaji suka shiga aikin ceto. A cewar Gwamnar tun da tsakaddaren jiya ne girgizar kasar ta fara wadda ta ce ta haddasa tsoro a zukatan al’ummar yankin.

Exit mobile version