Sagir Abubukar">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Sabuwar Dabara Ta Kusa Kawo Karshen ’Yan Bindiga – Mai Baiwa Gwamna Shawara

by Sagir Abubukar
January 14, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
'Yan Bindiga
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A kokarinta na kawo karshen matsalar tsaro da wasu kananan hukumomin jihar Katsina, ke fama da ita, kwararren masanin tsaro kuma mai bai wa Gwamna Aminu Bello Masari shawara kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina, ya ce, sabuwar hanya da suka bullo da ita za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da jihar ke ciki.

Ibrahim Katsina ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, a ci gaba da shirye-shirye wani taron karawa juna sani da ofishin sa zai shiryawa manema labarai a ranar alhamis mai zuwa.

samndaads

Gogaggen Masanin Tsaron, ya kara da cewa matsalar tsaro da muke fuskanta a jihar Katsina, tana bukatar nazari da bincike da kuma natsuwa. Idan aka rasa guda daga cikin wadannan ginshikai din yana da wahalar a kawo karshen ta. Saboda matsalar nan ba yau aka fara ta ba, kamar kansa ce kafin ta bayyana tana jikin dan Adam, lokacin da ta bayyana tana da wuya a magance lokaci daya. Gwamnati ta fara da binciken musassabin matsalar, bisa ga haka ne muke hadin-giwa da al’umma, shi yasa gwamna ya kai wata dokar sarakuna domin ayi Mata kwaskwarima ta a shigo da su don su ci gaba da bada guddumuwar kamar yadda suke a shekarun baya. Matsalar da muke fama da ita ta cikin gida ce, ba wai jami’an tsaro kadai ba ne za su kawo karshen ta ba. Bisa kokarin da al’umma ke yi to ya za’a yi a jawo al’umma ciki kuma tuni matakin ya fara haifar mana da da Mai ido, shi yasa kwanan nan hare-haren ma sun yi sauki kuma fahimtar ta fara daidaituwa.

Ibrahim Katsina ya ci gaba da cewa matakan da muka dauka na daidaita alammura na wadanda ke daji da wanda ake kaiwa hari za su zauna yadda za’a fahimci juna, an yi irin wannan a kasashen da suka cigaba. Yanzu haka yan bindigar sun fara gane muhimmancin zaman lafiya. Kura-kuran da muka yi a baya za mu gyara, akwai jahilci wajen su ya kamata malaman addinin Musulunci suna da rawar da za su taka, kamar yadda ta faru a jihar Kaduna. Saboda jihilci ya fi kafirci illa.

Mai baiwa gwamna shawara ya ce tsari ne bisa ga yi wa kowa adalci da turbar addinin Musulunci, bisa ga yafewa juna ba gwamnati za ta ce ta yafewa yan bindiga ba, su dai su nemi gafara al’umma da suke tare da su. Idan mun yi tsarin ba wai Katsina kawai ba, har sauran jihohi za su yi koyi bisa ga shimfida adalci. Ba za mu sa san rai ba, abinda muke so a yi mana kyakkyawa zato. Kofar mu a bude take na amsar korafe korafe da shawarwarin yadda za mu samu nasarar wannan aiki, harkar tsaro ta kowa ce kuma kowa na da guddumuwar da zai iya badawa.

Daga karshe, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana jin dadinsa bisa ga irin guddumuwar da al’ummar jihar Katsina ke badawa ta hanyar bada bayanan sirri ga ofishinsa. Wannan fitina ta kusa zama tarihi a jihar Katsina ta hanyar tuntuba da adalci.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa A Kotun Sojoji

Next Post

2023: Bindow Ya Nemi Mambobin APC Da Su Hada Kai

RelatedPosts

’Yan Sandan Italiya

’Yan Sandan Italiya Sun Kama ’Yan Nijeriya 16 Masu Sana’ar Miyagun Kwayoyi

by Sagir Abubukar
3 days ago
0

Rahotanni daga Kasar Italiya sun zo da ingacin cewa a...

miyagun kwayoyi

NDLEA Sun Cafke Mutum Uku Da Hodar Iblis A Legas

by Sagir Abubukar
3 days ago
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA),...

’Yan Fashi

’Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan Dan Uwan Akanta Janar Na ​​Imo

by Sagir Abubukar
3 days ago
0

’Yan sanda sun tabbatar da kisan dan uwan ​Akanta Janar...

Next Post
Muhammad Jibrilla Bindow

2023: Bindow Ya Nemi Mambobin APC Da Su Hada Kai

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version