Sabuwar Jam’iyyar BNPP Ta Shiga Da Kafar Dama A Yobe, In Ji Gishuwa

Shugaban sabuwar jam’iyar ‘Better Nigeria Progressive Party (BNPP) a jihar Yobe, Malam Ari Gishuwa ya bayyana cewa tana samun gagarumar karbuwa ga jama’a wadda ya ce ta shiga da kafar dama a kokarin ta wajen kawo canji a tsarin dimukradiyyar jihar.

Shugaban sabuwar jam’iyyar ya bayyana hakan a tattaunawa ta musamman da yayi da Leadership A Yau a Yobe. Wanda ya fara da shaidar da cewa jam’iyyar tana da kyakkyawan tanadi wajen inganta rayuwar matasa, inda ya ce” kamar yadda muka sani, matasa sune kashin   bayan kowacce al’umma, sannan duk al’ummar da ta gaza wajen dora matasan ta a turba mai kyau, ko shakka babu zata fuskanci kalubale da koma baya.” Inji shi.

Bugu da kari kuma, ya yi karin haske game da dalilan da ya sa suka kawo wa jama’ar jihar Yobe wannan sabuwar jam’iyya, tare da cewa sam ba su kawo ta da nufin musgunawa wasu mutane ba face kawai sai da nufin gyara, da ci gaba ta fuskacin siyasa.

Malam Ari yace “duk da dan Adam tara yake, bai cika goma ba, kuma bisa ga hakikanin gaskiya mun yaba da irin namijin kokarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kyautatuwar sha’anin tsaro, a yankin arewa maso-gabas, musamman kuma a jihar mu ta Yobe da Borno, wanda kafin hakan mun fuskanci matsanancin yanayi, amma yanzu al’amarin ya kyautatu. Kana da shirin gwamnatin tasa wajen yaki da cin hanci da rashawa”. Inji shi.

Bugu da kari kuma, wasu jama’a a jihar Yobe sun bayyana mabambantan ra’ayoyi dangane da wannan sabuwar jam’iyyar, daga ciki akwai Kyari Bamai Goni, mazaunin garin Dapchi cibiyar karamar hukumar Bursari a jihar Yobe inda ya kada baki ya ce “mu dama abinda muka dade muna jira kenan, domin gaskiya mun gaji da wannan danniyar da ake nuna mana da jimawa, kuma saboda yadda jam’iyyar mu ta APC ta yi ke watsi damu- ka ga dole mu nemi sabuwar tafiya; kuma muna tare daku dari bisa dari”. Inji shi.

Yayin da kuma wani tsohon dan jam’iyyar PDP a jihar (ya bukaci a boye sunan sa), dan kasuwa a garin Potiskum a jihar Yobe ya shaidar da cewa, shi kam tuni ya rigaya ya canja sheka daga tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP, tare da garzaya wa zuwa wannan sabuwar jam’iyya ta BNPP. Dan kasuwar ya shawarci Shugabanin wannan sabuwar jam’iyyar da cewa su kasance masu adalci a tsakanin yan jam’iyyar, domin gujewa kusa-kuran da sauran jam’iyyun suka tafka a baya.

 

Exit mobile version