Dr Masaud Kazaure, Sakataren gudanarwa na hukumar kula da makarantun kimiyya da fasaha ta kasa, wato NBTE a ranar Alhamis ya bayyana cewa sabuwar makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Daura a jihar Katsina, za ta fara aiki a zangon karatu na 2019/2020.

Dr Kazaure ya bayyana hakan ne a garin Daura a yayin da yake mika takardar shaidar mallakar filin da girmansa ya kai hekta 100 ga Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar wanda gwamnatin Katsina ta bayar.

Dr. Kazaure ya ce dukkanin wadansu shirye-shirye domin makarantar ta fara aiki tuni aka kaddamar da su ciki kuwa harda daukar ma’aikata. Ya tabbatar da cewa; ya zuwa yanzu suna da mutum 146 da suka nuna bukatar cike gurabe shida na manyan mukamin makarantar.

“Manyan mukaman da za a dauka domin fara gudanar da makarantar sun hada da; shugaban makarantar, magatakarda, mai kula da Laburare, Daraktan horaswa, Daraktan ayyuka, Sakataren karatu na makarantar.” In ji shi,

Ya yi kira da al’ummar garin da su ba da hadin kai da gudummawarsu wajen ganin makarantar ta fara aiki.

Dr Kazaure ya tabbatar da Sarkin cewa za a samar da nagartattu kuma kwararru wadanda a su gudanar da makarantar.

Dr Bishir Ruwangodiya mai bai wa gwamnan Masari shawara kan harkokin ilimin gaba da Sakandare, ya ce gwamnatin jiha ta sadaukar da karamar Sakandaren gwamnnati dake Daura domin wurin ya kasance makarantar na wucin gadi.

Ruwangodiya ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da gudummawarta domin ganin an cimma gaci dangane da makarantar.