Sabuwar Shekara: Dan Majalisa Ya Yi Kira A Kauce Wa Gudun Ganganci

A yayin da shagulgulan bikin Kiristemti da na sabuwar shekara ke kara karatowa, Dan Majalisar Dokoki na jihar kaduna Honorabil Auwal Mohammed Yahaya (yaro mai kyau) yayi kira ga masu amfani da hanyoyin kasar nan da subi doka da oda, domin kiyaye asaran rayuka da dukiyoyin al’umma a sanadiyar hadurra.

Dan Majalisar Honorabil Auwal Mohammed Yahaya ya yi kiran ne a hirrasa da manema labarai a Kaduna, inda ya yi nuni da cewa, sakamakon yin gudun ganganci da wasu masu ababen hawa ke yi musaman a motoci, hakan yana janyo salwartar rayukan matafiya.

Auwal Mohammed Yahaya  ya yi kira ga hukumar kiyeye hadurra ta kasa FRSC dake a jihar Kaduna da kuma ta kasa baki daya dagta sanya ido sosai akan irin direbobin dake yin gudun ganganci a lokacin bukukuwn da kuma bayansa don a hukunta direbobin dake karya ka’idar yin tuki, musamman akan manyan hanyoyin dake a fadin kasar nan.

Da ya ke yin tsokaci akan matan dake a daukacin fadin kasar nan, musamman a jihar Kaduna Dan Majalisar Honorabil Auwal Mohammed Yahaya shawarce su kada su gajiya kan irin gudunmawara da suka bayarwa wajen tabbatar da zaman a lafiya musamman a jihar Kaduna.

Dan Majalisar Honorabil Auwal Mohammed Yahaya ya yi nuni da cewa, sai da zaman lafiyar ne matakan gwamnati uku da ake dasu a kasar nan, musamman a Kaduna zasu damar amafana da romon dimokirayadiyya.

A karshe Auwal Mohammed Yahaya ya yi nuni da cewa, matasa sune manyan gobe a saboda hakan ya zama wajibi su dinga bin doka da oda, musamman a jihar Kaduna ganin cewar Gwmannan jihar Malam Nasir Ahmed el-rufai ya mayar da hankali wajen inganta rayuwar matasan dake jihar yadda zasu zamo masu dogaro da kansu.

A wata sabuwa kuwa, Rundunar kiyaye haddura dake a jihar Kaduna ta sanar da cewa, a basa yunkurinta na rage cunkoson a babane hawa a lokacin gudanar da shagulgulan Kiristimeti dana sabuwar shekara, a  kan hanyar Abuja zuwa Zariya, ta dauki kwararan matakai.

Kwamandan Rundunar, Hafiz Tarauni Mohammed, ne ya sanar da hakan, inda ya ce, ta samar da dabarun wajen bude wasu sassan hanyar da aka kammala aikin su dake a kan abbana titin na Kaduna   zuwa Zariya.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da DCC na Rundunar Salisu U Galadunci ya fitar.

Ya sanar da cewa, Rundunar ta dauki wannan matakan ne gannin yadda a lokacin shagulgulan babbar sallah data gabata matafiya sun sha wuya so sai akan babbar hanyar.

Exit mobile version