Sabuwar Shekarar Musulunci: Malaman Majami’u A Kaduna Sun Taya Musulmi Murna

Daga Abubakar Abba, Kaduna

A yayin da daucin Musulmi a fadin duniya suke ci gaba da bikin shigowar sabuwar shekarar Musulunci, malaman addnin Kirista a Jihar Kaduna, sun yi kira ga Musulmi a fadin duniya musamman na Jihar Kaduna, da su zauna lafiya da juna.

Malaman na addinin Kirista, sun yi kiran ne a jawabansu mabambanta a lokacin da kungiyar matasan Muslmi da ke jihar suka kai  ziyara a gidan sanannen fasto a jihar Pastor Yohanna Buru da ke Unguwar Sabon Tasha a Kaduna.

Tun farko a nasa jawabin, Pastor Yohanna Buru ya taya Musulmi shiga sabuwar shekarar ta Musulunci, ya kuma yi kira a gare su da kada su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya musamman a jihar don mara wa gwamnatin jihar baya wajen wanzar da zaman lafiya a jihar baki daya.

Buru ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan kasar nan, da su kara dukufa wajen yawaita addu’a don samar da hadin kan kasa. Dagan an, faston ya  shawarci matasan da su hada karfi da karfe wajen hada kai da sauran kungiyoyin matasa Kirista da ke jihar don kara tabbatar da dankun zomunci a tsakani.

Fasto Buru ya kuma bukaci mabiya addinan biyu, da su rungumi dabi’ar yafiya su kuma ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya don magance dukkan nau’uka na rikice-rikice.

Buru ya yi nuni da cewa, dukkan ‘yan-Adam a duniya sun fito ne daga

tsatson Annabi Adam da Matar sa Hauwa’u.

Ya kuma yi kira ga Musulmi dake fadn duniya da su tuna da gajiyayyu

lokacin shagulgulan sabuwar shekarar ta hanyar tallafa musu da ababen more rayuwa.

Shi ma da yake jawabi, Rabaran Titus Ishiaku, ya yi kira ga daukacin

matasa Musulmi da Kiristoci da ke kasar nan da su kauce wa furta kalaman kiyayya don kara tabbatar da zaman lafiya a kasar nan, musamman a Jihar Kaduna.

Jagoran tawagar matasan Malam Gambo Abdullahi Barnawa, sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa nuni ya yi da cewar, bikin sabuwar shekarar ta Musulunci, ba na Musulmi kadai ba ne, ya shafi daukacin wadanda ke doron kasa baki daya, tare da yaba irin tarabar da suka samu a wajen shugabannin na Kirista.

Exit mobile version