Sace Daliban Dapchi: ’Yan Sanda Za Su Yi Abinda Ke Neman Gagarar Sojoji

Daga  Muhammad Maitela, Damaturu

Mataimakin sufeto janar na ’yan sandan Nijeriya, Mista Joshak Habila, ya bayyana cewa, rundunar ’yan sandan Nijeriya a karkashin jagorancin Ibrahim Idris Kpotum za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an gano tare da dawo da ’yan matan Dapchi, wadanda a ke zargin ’yan kungiyar Boko Haram da sace su a makarantarsu ta kwana kwanakin baya kuma a ke ta faman korafin cewa har kawo yanzu sojojin kasar ba su iya ceto ba.

Babban jami’i a rundunar ’yan sandan ya bayyana cewa, jami’an tsaro su na kara daukar sabbin matakai da dabarun da za su kai ga nasarar yadda za a ceto daliban makarantar Dapchi da a ka sace a jihar ta Yobe.

Mista Habila ya bayyana hakan ne a sa’ilin da ya ke zanta wa tare da manema labarai a Damaturu, inda ya ce ya zo jihar Yobe domin domin haduwa da gwamnati hadi da masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi a jihar.

“Mun yi taron ne domin lalabo matakan bi da za su kai ga nasarar ceto ’yan matan tare da karin wasu dabarun dauka kan lamarin daban-daban, kana da yadda za a samu cikakken tsaro a makarantu da kokarin kauce wa duk abinda zai kawo cikas a sha’anin karatun,” in ji Habila.

Ya kara da cewa, ’yan sanda tare da hadin gwiwa da jami’an tsaron Civil Defence sun riga sun tuttura jami’an tsaro a makarantun jihar.

Bugu da kari kuma ya ce, wannan taron zai kunshi kwamishinan ilimi a jihar, manyan jami’an ma’aikatar ilimin, shugabanin manyan makarantu, shugabanin makarantun sakandire da na firamare tare da malaman makarantu a jihar Yobe.

Haka zalika kuma, Mataimakin Sufeto Janar din ya bukaci jami’an ’yan sanda da kanana da ke jihar kan su bayar da himma wajen gudanar da ayyukan da ke gabansu, domin kaiwa ga samun cikakken tsaro a jihar Yobe.

Har wa yau kuma ya ankarar da ’yan sandan kan cewa su yi kokari wajen gina kyakyyawar alaka ta gaskiya tsakanin su da jama’a wanda hakan zai sahale mu su hanyar samun sahihan bayanan sirri da zasu basu damar dakile irin wannan ta’asa wadda ta afku.

Kana kuma ya kara jaddada muhimmancin gudumawar al’umma a aikin dan sanda ta fuskar gina kyakkyawar alaka tsakanin ‘yan sanda da jama’a wajen samun tsaro.

…Iyayen Daliban Dapchi Sun Yi Zanga-Zanga Abuja

Wasu daga cikin iyayen dalibai 110 da a ka sace a makarantar GGSTC Dapchi a jihar Yobe tare da hadin gwiwa da kungiyoyin fafutuka sun gudanar da zanga-zanga a farfajiyar majalisar dokoki ta kasa, inda su ka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kwato mu su ’ya’yansu.

Masu zanga-zangar, wadanda mafi yawan su ke sanye da bakaken kaya tare da gamayya da kungiyoyin fafutuka irin su ‘Coalition in Defence of Nigerian Democracy and Constitution’ da hadin gwiwa da ‘Our Mumu DonDo Movement’.

Jerin gwanon ya kunshi biyar daga cikin iyayen daliban guda biyar daga Dapchi zuwa babban birnin tarayya na Abuja. Uku daga cikin iyayen, wadanda su ka zanta da manema labarai, sun bayyana yadda bacci ya yi kaura daga idanunsu tare da rashin jin dandano daga harshensu tun bayan sace yayan su da mayakan Boko Haram su ka yi a sa’ilin da su ke dakon jin duriyar ’ya’yansu.

Daya daga cikin iyayen, Yahaya Tarbutu, mai kimanin shekaru 45 a duniya, ya bayyana yadda lamarin ya rutsa da yayan sa guda biyu daga cikin ’yan matan da aka sacen. Ya ce a halin da a ke ciki yanzu, rayuwar sa ta tashi daga duniyar farin ciki zuwa wata duniya ta matsanancin damuwa, tun ranar 19 ga Faburairun da aka tafi da daliban makarantar.

’Ya’yan nasa su ne Fatima Tarbutu mai shekaru 13 da Amina Tarbutu ’yar shekara 14, yayin da kuma ya yi sa’ar gano dayar, Maryam Ahmed, mai shekaru 15 a duniya, wadda kuma marainiya ce da ya ke riko.

Malam Tarbutu ya ce, “sam ba na jin dadi a rayuwata, tuni bacci ma kokari ya ke ya kaurace wa idanu na, sannan harshe na ya rasa jin dandano. Tun a sa’ilin da na kira mataimakin shugaban makarantar kan lamarin sace yaran, tare da bani tabbacin cewa Boko Haram sun shiga dakin kwanan daliban. Tun daga wannan rana rayuwata ta ke cikin tsanani”.

“Wanda kuma a kashe gari, ni da sauran iyayen dalibai mun shiga makarantar tare da kutsa kai cikin daji ko Allah zai sa mu gano wadanda suka gudun. Wanda kuma a haka muka yi sa’ar gano wasu yan matan, inda muka rasa sauran. Alhalin wadanda muka gano din suka tabbatar muna cewa an yi awon gaba da sauran”. Inji shi.

Bugu da kari kuma, a wannan ranar saida daya daga cikin iyayen, Malama Fatima Saleh, ta fada rashin lafiya yayin da har aka garzaya da ita zuwa asibitin Asokoro dake Abuja.

Malama A’isha Bukar, uwa ce ga daya daga cikin daliban da aka sacen inda kuma ta ce yarinyar wadda take gab da kammala sakandiren (Senior Secondary: Class 2A), tayi karin hasken cewa ita kam tuni ta nada gammo da rungumi kaddara.

Ta bayyana cewa, “sun sace ‘ya ta wadda take ajin babbar sakandire na SS2A. Kuma tun daga wancan lokacin muka yi rabon makaho da kuturu da bacci. Karawa da karau, babu wani jami’in tsaron da ya taba tattauna lamarin damu. Muna bukatar gwamnati ta kwato muna yayan mu. Ni matar aure ce, bana aikin gwamnati, na damu matuka da rashin ya ta”. Ta ce.

“Ba mu da wata masaniya dangane da yuwuwar zuwan mayakan Boko Haram a makarantar, kawai sun zo muna ne cikin rashin sani. Sun zo tare da harbin kan mai uwa da wabi, kuma basu bar Dapchi ba sai wajen karfe 8:30 na dare,” in ji ta.

 

 

Exit mobile version