Sace Daliban Jami’a A Kaduna: Yadda ‘Yan Bindiga Suka Shammaci Jami’an Tsaro

Suna Neman Kudin Fansa Naira Miliyan 800

Daga Abubakar Abba, Kaduna

A daren ranar Talata da dare ne wasu ‘yan garkuwa da mutane dauke da makamai suka shammaci jami’an tsaro suka afka wa wata jami’a mai zaman kanta da ke Jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da wasu dalibai.
Jami’ar mai suna Green Field University tana kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, a yankin karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Jami’ar dai ita ce ta farko mai zaman kanta da aka kafa a jihar a cikin shekaru uku da suka gabata.
Sabon harin a daya daga cikin cibiyoyin ilimi na jihar ya zo ne yini daya bayan Gwamnan Jihar Kaduna ya nanata matsayinsa a wani taro a Abuja cewa a darkake ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane matukar ana so makarantu su zauna lafiya.
Haka nan harin na wannan lokacin shi ne mafi muni da ‘yan bindigan suka kaddamar a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja tun bayan da aka tura dakarun soja mata guda 300 a yankin, a cikin watan Janairun wannan shekarar.
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai.
Wani ganau ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun afka wa jam’ar ne a daren ranar Talata inda suka yi ta harbe-harbe ba kakautawa kafin su sace daliban.
Su kuwa wasuu makwabtan jami’ar sun bayyana cewa, daliban jami’ar ba su da wadataccen tsaro, kuma ga shi jami’ar ta kasance a yankin da lamarin sace mutane ya yi kamari, inda suka yi nuni da cewa, hakan ya bai wa ‘yan bindigan damar cin karensu ba bu babbaka da kuma kutsawa cikin jami’ar cikin sauki.
Idan za a iya tuna wa, har yanzu dai akwai ragowar dalibai 29 daga cikin dalibai 39 na makarantar koyon aikin gandun daji da ke a Afaka a cikin karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna da ‘yan bindiga suka a ranar 11 ga watan Maris na wannan shekarar.
A jiya Laraba an ruwaito Kakakin Rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, yana tabbatar da afkuwar lamarin, inda kuma ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun kuma harbi wani ma’aikacin jami’ar baya ga garkuwa da da daliban.
A cikin sanarwar da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya fitar ya bayyana cewa dakarun soji na rundunar OPTS da sauran jami’an tsaro a jihar sun gaggauta zuwa jami’ar amma ‘yan bindigan sun riga sun arce da daliban.
A cewarsa,  sauran daliban da ba a sace ba sun samu kulawar jami’an tsaro, inda daga bisani aka mika su ga hukumar jami’ar a jiya Laraba.
A halin da ake cikin kuma, masu garkuwan da suka sace daliban na Jami’ar Green Field sun tuntubi iyayensu, inda suka bukaci a ba su naira miliyan 800 a matsayin kudin fansa kafin su sako su.
Wata Majiya ta bayyana cewa, daliban jami’ar guda 23 ne aka sace, inda zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ana ci gaba da tattaunawa da masu garkuwar da iyayen daliban.
An ruwaito daya daga cikin ‘yan uwan daliban da aka sace Misis Georgina Stephen tana bayyana cewa, masu garkuwar sun bukaci ta biya Naira miliyan 8 a matsayin kudin fansar kanwarsu.
Georgiana ta kara da cewa,  daliban su 23, sun hada da mata  14 da maza 6 da kuma wasu ma’aikatan jami’ar.
A cewarta, masu garkuwar suna ta dukan daliban kan cewa, sai an biya su kudin fansa su sake su, idan kuma ba a biya ba za su kashe su.

Exit mobile version