Sace Daliban Kankara: Wasan Kwaikwayo Gwamnatin Katsina Ta Shirya, Cewar Mahdi Shehu

Mahdi Shehu

Daga Ibrahim Ibrahim, 

 

Bayan tataburzar da ta faru tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da sanannen Dan Kasuwar nan mazaunin Garin Kaduna, kuma Dan asalin Jihar Katsina Dakta Mahadi Shehu, Dan Kasuwar ya tabbatar da cewar yanzu aka fara sabon lale tsakanin shi da Gwamnatin Jihar Katsina.

Idan dai ba’a manta ba, A kwanakin baya ne dai jami’an tsaro bisa ga umarnin Gwamnatin Jihar Katsina suka kama Dakta Mahadi Shehu, inda aka garzaya dashi Birnin Tarayya Abuja, ya fuskanci gagarumin kalubale da suka hada da barazana ga rayuwar shi da sauran abubuwan da suka faru na tashin hankali a gareshi.

Daga bisani Dakta Mahadi Shehu ya yi nasara akan Gwamnatin Jihar Katsina a karar da ta shigar a kanshi, inda Kotun daukaka kara ta wanke shi daga dukkanin zarge-zargen da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi mishi.

A zantawar da ya yi da manema labarai a ofishin shi dake Kaduna, Dakta Mahadi Shehu, ya tabbatar da cewar ko kadan bai razana da barazanar da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi mishi ba, kuma a halin yanzu ne ya sake damarar ci gaba da fallasa irin waka ci ka tashi da ake yi da dukiyar jama’ar Jihar Katsina da watsi gami da nuna ko in kula akan rayuka da dukiyoyinsu.

Dakta Mahadi Shehu wanda ya koka da shiru da manyan Malamai a Jihar Katsina suka yi akan tabarbarewar tsaro a jihar, Malaman da a baya suka yi ma wannan gwamnati kamfe da la’antar gwamnatocin baya na PDP, lallai wannan abin takaici ne da bakin ciki kuma tabbas mutuncin wadannan malamai ya zube warwas a idanun jama’ar Jihar Katsina.

Dakta Mahadi Shehu ya sha alwashin ci gaba da fallasa zaluncin Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Masari da Sakataren Gwamnatin Jihar Mustafa Inuwa, da kuma ‘yan kanzagin su, kuma a shirye yake ya fuskanci dukkanin wata barazanar da za’a yi mishi ko da zata kai ga rasa ranshi ne.

Dangane da batun sace daruruwan Daliban Makarantar kimiyya ta Kankara da aka yi, tare da sako su ba tare da bata lokaci ba, Dan kasuwar ya bayyana hakan a matsayin wani wasan kwaikwayo da Gwamnatin Masari ta shirya, kuma da yardar Allah asirin su zai tonu.

Daga karshe Dakta Mahadi Shehu ya yi kira ga jama’ar Jihar Katsina da Nijeriya baki daya, da su dage da yin addu’o’i akan Allah ya yi musu maganin miyagun Shugabanni wadanda ke cutar su da zaluntar su, kuma da yardar Allah gaskiya za ta yi halinta, domin zalunci har abada ba zai taba dorewa ba. A cewarsa.

 

Exit mobile version