Yusuf Shuaibu" />

Sadarwa Na Da Matukar Mahimmanci Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Nijeriya – Danbatta

danbatta

Shugaban hukumar kulawa da harkokin sadarwa a Nijeriya (NCC), Farfesa Umar Danbatta ya bayyana cewa, harkokin sadarwa yana da matukar mahimmanci wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan. Farfesa Danbatta ya bayayana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taro da ya gudana a kwalejin tsaro ta kasa.

Ya ce, “kamfanonin sadarwa da ke karkashin kulawar hukumar NCC suna taka mahimmiyar yawa wajen bunkasa tattalin arzikin zamani. Bangaren sadarwa yana matukar samar wa gwamnatin tarayya kudaden shiga.”

Ya kara da cewa, bangaren yana taka rawa guda biyu wadanda suka hada da samar da kudaden shiga da kuma bayar da dama ga sauran bangarorin tattalin arziki.

“Fannin sadarwa yana da matukar mahimmanci wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya, inda bangaren yake samar da haraji mai yawan gaske da kuma bai wa sauran bangararorin tattalin arziki daman samun kudaden.

Ya ci gaba da cewa, bangaren sadarwa ya samu nasarar zuba kudaden haraji wadanda suka kai na naira biliyan 362.34 a asusun gwamnatin tarayya a cikin shekara biyar. Ya ce, bangaren sadarwa yana rage tazara na ababan more rayuwa wanda yake saukaka samun abubuwa cikin sauki, wanda ko mutane suka zaune a cikin gidajen su za su iya sayan katin wutar lantarki, sannan sashin ya yi kokarin magance duk irin matsalolin da ya fuskanta a baya.

A nasa bangaren, shugaban kwalejin tsaro da kasa, Rear Admiral Mackson Kadiri ya yaba wa jawabin shugaban hukumar NCC, bisa yadda ya dauki tsawon lokacin yana gudanar da jawabai masu daukan hankali da kuma rawar da fannin sadarwa ke takawa a cikin bangaren bunkasa kasa.

Exit mobile version