Safarar Mutane: Dogara Ya Jagoranci Wakilan Nijeriya Zuwa Italiya

Daga Abubakar Abba

Kakakin Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara, ya jagoranci wata babbar tawaga ta musamman zuwa ƙasar Italiya, don tattaunawa akan yadda za a rage talauci tsakanin mata da kuma yaƙi da safarar mutane wadda take ƙara zamowa ruwan dare a wasu sassan na duniya.

Ziyarar ta zo dai-dai kan gaɓa, bayan mutuwar mata ‘yan Nijeriya su 26 a cikin wani jirgin ruwa, lokacin da suke kan hanyar su tsallaka wa ƙasar Italiya ta ɓarauniyar hanya.

Gwamnatin ƙasar ta  Italiya ce, ta gayyaci Dogara ya halarci taron na ƙasa -da-ƙasa, don rage talauci a tsakanin mata da yaƙar safarar mutane.

Haɗakar tsakanin Nijeriya da ƙasar ta Italiya, za a gudanar da ita ne Birnin Rome.

Bugu da ƙari, hakan ya biyo bayan ziyarar aiki da Shugaban Majalisar Ƙasar Italiya Laura Boldrini ta kawo wa Honorabul Dogara a cikin watan Mayun shekarar 2017.

Gwamnan jahar Edo  Godwin Obaseki da Darakata- Janar na Hukumar Haramta Safarar Mutane NAPTIP, Uwargida Julie Okah-Donli suna daga cikin tawagar.

Tawagar zata halarci taron gayyatar da majalisar ta ƙasar Italiya ta yi mata, da nufin yin haɗaka da Nijeriya da ƙasar Italiya, don kawo ƙarshen yin safarar mutane, musamman yadda ake ƙara samun ƙaruwar yawan ‘yan Nijeriya da suke tsallakawa Italiya ta kan Teku Mediterranean a duk shekara.

Lokacin da Laura ta kawo Dogara ziyarar, a cikin watan Mayu na wannan shekarar, ta koka akan cewar, a shekarar 2016 kacal, ‘yan Nijeriya su 37,000 suka shiga ƙasar Italiya ta hanyar Tekun Mediterranean.

A tattaunawar da za a yi lokacin taron, za a samar da hanyoyin da za a rage talauci musamman a tsakanin mata don su daina yawaita yunƙurin tsallaka wa ƙasar Italiya ta ɓarauniyar hanyar da ke da haɗarin gaske.

Exit mobile version