Safiya Umar Badamasi ita ce mace ta farko ‘yan kabilar Hausa/Fulani kuma Musulma da ta kai matsayin babbar lauyar Nigeriya,(SAN) kuma ita ce, lauya ta farko da ta kai ga irin wannan matsayin a dukkan fadin jihar Katsina.
Safiya na daya daga cikin lauyoyi dari da goma sha bakwai wadanda suka nemi wannan matsayi a bana. An ware mutum tamanin wadanda aka jera sunansu, amma a karshe aka zabi mutum talatin da takwas ne aka tabbatar musu da wannan matsayin a bana.
A tattaunawar da suka yi da jaridar DAILY NIGERIAN, Malama Safiya, ta nuna farin cikinta bisa tarihin da ta kafa a fannin ilimin mata a matsayinta na Musulma ‘yan Arewa.
Malama Safiya ta ci gaba da bayanin cewa, ta samu karfin gwiwar yin karatu ta hanyar samun shawarwar da malaminsu. Saboda sai na dage sosai a kan bangaren darasin Tarihi da Adabi tun ina sakandire. Na samu sakamako mai kyau a wadannan darusa, don haka aka ba ni shawarar in karanta shari’a. Ta ce, kasancewarta babbar lauyar Nijeriya a jiharta, za ta zauna a jihar Katsina domin ta ci gaba da karfafa lauyoyi masu tasowa.
“ Na zabi in zauna a Katsina domin in kawo ci gaba a jihata kuma in koyawa lauyoyi masu tasowa maimakon in tafi wani wuri domin in samu kudi,” in ji ta.
An haifi Malama Safiya ranar 12, ga watan Yuni, 1968, a garin Malumfashi da ke jihar Katsina ta fara ta rike matsayi daban-daban a ma’aikatar shari’a ta jihar Katsina.
Ta yi karatunta na firamare a makarantar firamare ta Aya ta ke Funtuwa, kuma ta gma inda ta samu takardar shaidar kammalawa a shekara ta 1980.
Ta wuce zuwa FGCC Bakori, Katsina daga shekara ta 1981 zuwa 1985. Ta fara karatun shari’a a shekara ta 1985 a Kwalejin koyon shari’a da ilimin addinin Musulunci wadda a yanzu ta koma Hassan Usman Katsina Polytechnic inda ta samu Difuloma a fannin shari’a a shekara ta 1987.
Daga nan ta wuce zuwa jami’ar Bayero da ke Kano daga shekara ta 1991 suwa 1995, inda ta samu digirinta na farko a fannin shari’a wanda ya ba ta dama ta je makarantar lauyoyi da ke tabbatar da wanda ya kamamla karatun shari’a, wadda kuma daga nan ta zama lauya a kotun koli ta Nijeriya a shekara ta 1998.
Malama Safiya ta fara aiki a Ma’aikatar kasuwanci da yawon shakatawa ta jihar Katsina daga shekara ta 1989 zuwa 1990 a matsayin jami’a mai kula da sashin yawon shakatawa.
Daga nan ta koma ma’aikatar shari’a ta jihar ta Katsina inda ta kai ga matsayin babbar sakatariya kuma babbar lauyar gwamnatin jihar Katsina.
Kafin ta zama babbar lauyar gwamnatin jihar Katsina, ta rike matsayin daraktan kula da korafe-korafe na jam’iyyar DPP, a jihar Katsina daga shekara ta 2007 zuwa 2018.
‘Yan Sanda sun Kama Wanda Ya Kashe Mahaifinsa A Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar da cewa, ta kama wani matashi, mai suna Jamilu Harisu, dan shekara 25, bisa zargin kashe mahaifinsa mai kimanin shekara 70, a jihar Jigawa. Wanda ake zargin ya aikata wannan danyen aikin ne, a lokacin da ya sha kwaya, kuma ya far wa mahaifin nasa da sara a gona.
Harisu ya kashe mahaifin nasa ne a kauyen Makku da ke karamar hukumar Garki ta jihar Jigawa, bayan ya sassara masa fatanya. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar SP Audu Jinjiri, ya tabbatar da mutuwar marigayin a asibitin Garki Hospital. “Tuni dai ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin da laifin kisan kai. An kuma bayar da umarnin cewa, a mayar da kes din zuwa sashin bincike, domin gudanar da cikakken bincike kan wannan al’amarin.”