Sai A Karshen Kakar Wasa Za A San Matsayar Manyan Kungiyoyi A Firimiyar Ingila

Canja ’Yan Wasa

Daga Abba Ibrahim Wada

Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Sol Campbell, ya bayyana cewa sai ranr  za’a kammala buga wasannin gasar firmiya sannan za’a san matsayin wasu daga cikin manyan kungiyoyin da suke buga gasar musamman masu neman gurbin kofin zakarun turai.
kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wadda take ta biyu akan teburi taje har gida inda ta lallasa Tottenham da kwallaye 3-1 a wasan ranar Lahadi da suka fafata na gasar Firimiya.
Tun da farko dai Tottenham ce ta fara jefawa Manchester United kwallo a raga ta hannun dan wasanta Son Heung-min, daga bisani kuma Fred, Edinson Cabani da Mason Greenwood suka  ciwa Manchester United na ta kwallayen uku.
A halin yanzu Manchester United ta rage tazarar maki 14 da Manchester City mai jagorantar gasar Firmiya ta ba ta, inda a yanzu ya koma 11, bayan da Manchester City ta sha kaye a wasan da Leeds United ta doke ta da ci 2-1 har gida.
kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kuwa zuwa tayi har gida itama ta doke kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace da ci 4-1 ya yinda Leceister City tasha kashi itama a hannun kungiyar West Ham United.
Har yanzu Manchester City ke jagorantar frimiya da maki 74, sai Manchester United da maki 63, sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Leicester City da maki 56 sai kuma kungiyar Chelsea a mataki na hudu.
A can kasa ajin ‘yan dagaji kuma kungiyar kwallon kafa ta Fulham ce ta 18 da maki 26, sai kungiyar West Brom na da maki 21 a matsayi na 19, sai ta karshe Sheffieled United wadda Arsenal ta doke har gida da maki 14.

Exit mobile version