Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiyar kungiyar Paul Pogba zai ci gaba da jinya har bayan watan Fabrairu, ba zai buga wa kungiyar wasa da Real Sociedad ba.
Wasu ‘yan wasan da ba su yi wa Manchester United gasar zakarun Turai ta Europa League ranar Alhamis ba sun hada da Donny Ban De Beek da kuma Edinson Cabani wadanda duka suke fama da ciwo.
Manchester United ta ci gaba da buga gasar Europa League wasannin kungiyoyi 32, bayan da ta yi ta uku a cikin rukuni a gasar cin kofin zakarun turai wato Champions League a bana wanda hakan yasa ta dawo gasar Europa.
Kungiyar ta Old Trafford ta buga karawar a Turin wato filin wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus maimakon San Sebastian, bayan da Spaniya ta sa dokar hana shiga kasarta don gudun yada cutar korona.
Kawo yanzu Pogba ba zai buga wasan da Manchester United United za ta kara da Real Sociedad a Italiya da wanda za su fafata a filin wasa na Old Trafford ba a gasar ta Europa League ta wannan shekarar.
Haka kuma dan kwallon ba zai yi wa kungiyar wasan da za ta yi gumurzu da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ba da kuma wanda zata fafata da Chelsea, sannan watakila ba zai je Etihad wasan hamayya da Manchester City ba.