Umar A Hunkuyi" />

Sai A Watan Yuni Zan Sauka Daga Kakakin Majalisa — Dogara

Dogara

Kakakin Majalisar Wakilai ta kasa, Yakubu Dogara ya ce, wa’adin Majalisar ta wakilai mai ci a halin yanzun zai ci gaba da kasancewa ne har zuwa nan da wasu watannin uku, ya kara da cewa, akwai mahimman abubuwa da suka saura a gaban Majalisar a halin yanzun.
Dogara ya fadi hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin manema labarai, Turaki Hassan, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Kakakin ya ce, daga cikin mahimman abubuwan da suka saura a gaban majalisar da suke bukatar a gaggauta tattauna su akwai kasafin kudi na wucin gadi na 2019.
“Kakakin ya mayar da hankali ne kan alkawarin da Majalisar ta yi na kammala duk aikin da ke gabanta a cikin Majalisar ta wakilai.
“Batun wa zai zama abu kaza a zaman Majalisar hawa na 9, sam ba shi ne a gaban shugaban Majalisar na yanzun, Yakubu Dogara ba.
“Zai fi kyau ku rabu da shi daga wadannan zace-zacen da ba su da tushe,” in ji Turaki.
Wasu kafofin yada labaran sun kawo rahotanni kan ko su wane ne a sahun gaba wajen samun shugabancin majalisar a cikin Majalisun biyu

Exit mobile version