“Sai An Biya Naira Miliyan 200 Sannan Za Mu Sako Sarkin Kajuru”

Daga Sulaiman Ibrahim

Wadanda suka sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, sun nemi kudin fansa Naira miliyan 200.

An sace sarkin tare da wasu danginsa 13 daga gidansa da ke garin Kajuru a safiyar ranar Lahadi.

Daya daga cikin masu rike da sarautar masarautar ya tabbatar wa manema labarai cewa ’yan bindigar sun tuntube su don biyan Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa.

A cewarsa, ana ci gaba da tattaunawa.

Exit mobile version