Sai An Cire Kwadayi San Nan Dimokradiyya Za Ta Zauna Daram A Nijeriya -Dan Sa’a

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

An tabbatar da cewar, sai an cire kwadayi da kuma son raid a kuma kabilancin harshe da kuma na addin, san nan Dimokradiyya za ta zama mai amfani ga al’ummar kasar nan.

Wani fitaccen dan siyasa day a fara siyasarsa tun a zamanin jamhuriyya ta farko, mai suna Alhaji Aliyu Dan Sa’a da ke Unguwar Kaura a birnin Zariya ya bayyana haka a zantawarsa dawakilinmu da ke Zariya.

Alhaji Aliyu Dan Sa’a ya ci gaba da cewar babu abin day a lalata Dimokradiyyar da ake ciki a yayu sai abubuwan da aka ambata,wanda kuma ya ce a jamhuriyya ta farko da kuma ta biyu babu wadannan abubuwa da aka ambatagaba daya, sai mai za a yi a ciyar da al’ummar Nijeriya gaba a ko wane bangare.

Fitaccen dan siyasar ya kara da cewar,a jamhuriyya ta farko, babban abin da aka saw a gaba shi ne, duk wanda ya shiga takara ya ya halayensa suke wasu ire-iren gudunmuwa yak e bayarwa a cikin al’ummar day a fito, amma baya ga wadannan abubuwa, a cewarsa, babu wani abu da ake dubawa, har ya zuwa dan siyasa ya kai ga nasara a duk takarar da ya shiga a ko wane mataki na zabe.

Alhaji Alyu Dan Sa’a, ya kara da cewar, a yau abubuwan da ake sa wa a gaba su ne, me dan takara ya ke da shi na kudi, da kuma yawan kudin day a tanada domin raba wa jama’a a lokacin tafiya yakin neman zabe tare da al’umma da suke rufa ma sa baya, duk mutuncinsa a cikin al’umma, in ba shi da kudin da zai shiga takara,  dole ya hakura da takarar da ya fara.

Fitaccen dan siyasar ya bayar da misali da a lokacinsu, na har dan takara ya fara takara ya kai ga samun nasara, ba a tambayarsa ko da kwabo daya da sunan abin da za a ci a tsawon raka shi yakin neman zabe a tsakanin al’umma.

Da kuma yak e tsokaci na yadda a yau shugabannin jam’iyya ba su da daraja a idon ‘yan takara, Alhaji Aliyu Dan Sa’a ya ce, sanya kwadayi ga ‘yan takara ke yi, shi ne kan gaba na yadda dan takara a yau ya mayar da su gugar yasa, suna da amfani kafin zabe, bayan zabe kuma an manta da su, wannan ne ke sa a yau shugabannin jam’iyya ba su da mutunci a idon duk wani zababbe, domin mafiya yawansu, sun nuna kwadayinsu, kafin zabe a tsakaninsu da ‘yan takara ko kuma dan takara.

Wannan matsala, a cewarsa a yau shugabannin jam’iyya ba su da mutuncin da za su yi kirar zababbe ya je garesu, sai dai shi ya kira su, su kuma je wajensa a guje.

A karshe Alhaji Aliyu ya ce ,a lokacinsu babu wannan matsala ko kuma kwadayi a tsakanin shugabannin jam’iyya, suna kirar duk wani zababbe a duk lokacin da suka ga dama, ya je garesu a lokacin da sukae bukata.

Exit mobile version