Ibrahim Muhammad" />

Sai An Hana Shigo Da Tumatur Sannan Za A Samu Habakar Harkar A Kasar Nan -Alhaji Abdulkarim Kaita

Sakamakon kuka da game da asararda Manoman tumatir ke yi bayan sun noma saboda rashin samun ciniki daga kanfanoni da sune ke saye su sarrafashi. Masana’antan Dangote dake Garun Malam a jahar kano daya ne daga kanfanin da aka yi dan saye da sarrafa tumatir da ake nomawa a Kano wanda yanzu jaka kanfanin ya dakatarda aikinsa sakamakon asara da suke fuskanta su ma. IBRAHIM MUHAMMAD ya sami tattaunawa da Manajan Daraktan masana’antar sarrafa tumaturin na Dangote ALHAJI ABDULKAREEM KAITA akan irin matsalolin da suke fuskanta a harkar ga yadda hirar ta kasance:

Me za ka ce game da kukanda manoman tumatir suke na cewa suna tafka asara saboda rashin kasuwa daga irin masana’antunku da kuke saye dan sarrafawa?

Kowa ya san yadda ake noman tumatur ya san irin asarar da manoma ke yi, dalilin wannan muka kafa wannan masana’antar dan tallafa musu su rage asara amma me zai faru, tumaturin da ake shigowa dashi daga kasashen waje, kasar Chana da sauransu suna shigo dashi ne na daya dai gurbatace ne, saboda haka ana shigo da shi da araha sosai, idan mun sayi tumaturin nan wajen manoma mun sarrafa ba wanda zai saya a hannunmu domin su wadanda ya kamata su saya hannunmu suke shigowa dashi daga kasashen waje.

Saboda haka idan ba an dauki wani mataki ba da zai dakatar da shigo da tumatur daga kasar waje ba yadda za a yi mu saya a wajen manoma mu sarrafa kuma muma mu sayar. To a dalilin haka shi yasa masana’antun nan akaga bamu kadai ba, akwai su Ikara, su Gombe duk a rufe suke dan ba yadda za a yi su siyi tumatur wajen manoma kuma su sarrafa kuma su sayarwa wadandanan mutanen masu shigo dashi ba zai yiwu ba.

Wane irin kalubale za a iya fuskanta in aka cigaba da shigo da tumaturin kasar nan duk da muna da masu nomata a cikin gida?

Tun sanda Gwamnatin Shugaban kasa Buhari ta shigo babban abin da suka ce za su habaka shi ne noma, to wannan yaba kowa dake harkar noma kwarin gwiwa cewa lallai yanzu noma zai albarka an gani sunyi a shinkafa an hana shigo da ita kuma manoman shinkafa da masu kafa masana’antun sarrafa shinkafa an tashi an habaka, yanzu labarin shigo da shinkafa an soma mantawa da shigo da ita, abin da mu ke so kenan Gwamnati ta yi wa manoman tumatur, kasar nan za mu iya noma tumaturin nan har ma mu sayarwa wasu kasashe, saboda haka ba mu ga dalilin da zai sa a rika bari ana shigo da ita ba. Ana kashe kwarin gwiwar manomanmu na tumatur kullum ana sasu suna asara, mu da muka kafa masana’antu mu an samu mun rufe masana’antun nan muna ji muna gani kullum asara.

To dakatar da aiki da kukayi na sarrafa tumatur a masanakantarku yanada alaka kenan da shigo da tumatur da ake yi?

Eh, kwarai kuwa, dan abin da ke faruwa ka ga mu ma’aikatarmu tana sarrafa tumaturine a cikin duro ba’a cikin kananan gwangwani ba, kuma irinsa shi ne ake shigowa dashi daga Chana sai susa a leda da gwangwani. Mu niyyarmu mu rika sayarwa wadanda ke sayowa daga chana dan a daina shigo dashi, to ka ga su suna shigo dashi da araha, saboda haka su mu ke so su saya daga wajenmu, mu kuwa akwai farashinda ba za mu iya sayen tumatur ba, idan ya wuce haka, tunda ko mun saya mun sarrafa sai dai mu yi asara ba za su saya ba, babbar matsalar kenan da ake fuskanta.

To dole dai tasa kenan kuka daina aikin?

Dole ta sa muka daina aiki.

Saboda tumatir idan manoma suka noma ku zaku saya ku sarrafa?

Mu za mu saya kuma in yayi tsada, muka saya muka sarrafa su wadanda muke ganin za su saya daga hannunmu za su ce a’a ya yi musu tsada gara su saya daga waje.

Kun taba kai korafinku ga Gwamnatine akan ta dauki mataki na hana shigowa da tumatur tunda dai ana nomawa anan kasar?

Eh, mun kai kuka ga Gwamnati wajen kusan shekaru Uku kenan a na ta ja-in-ja daga karshe dai Gwamnati ta amince taga yadda a ke yi wa noman tumatir a kasar nan, to amma maimakon asa takunkumi na hana shigo dashi gaba daya sai suka ce to daga yanzu a daina shigo dashi takan iyakoki na kasa sai dai ta ruwa. Kuma suka ce duk wadanda suke shigo dashi ta kananan gwangwani ko leda suma an daina, sai wanda za su shigo da shi a duro.

Wannan ya nuna ba a fita ba kenan?

Ba a dai fita din ba kenan har yanzu ana nan, saboda haka yanzu su kansu manoma su abin da ke damunsu suna noma tumatur suna asara, idan sun zo sun same mu, mu ce musu mu kuma bamu iya saye, idan mun saya ba wanda zai saya wajenmu

Kana ganin hakan ya taimaka wajen dakile samar da aikin yi kenan?

Kwarai ma kuwa ga ma’aikatarmu dole mun rufeta wajen shekara Uku, ma’aikatan da muka dauka duk mun sallame su.

Akalla kuna da ma’aikata nawa a lokacin?

Muna da ma’aikata da suke aiki a “Factory” Kamar mutum 150 saboda haka shi ne su kansu manoman suke kuka da Gwamnati cewa garama a dakatarda shigowa da tumatur gaba daya tunda takunkumin da a ka sa baya tasiri, idan ba an dakatar ba ne kamar yadda aka yi na shinkafa. Ka ga yanzu shinkafa an hana shigo da ita kuma ga ta nan ana nomata manoma suna samun alkhairi yadda ya kamata kuma kanfanonin sarrafa ta dada habaka suke. Ballantana tumatur dako ba ka da gona za ka iya nomata a cikin gidanka wannan shi ne babban kalubale da ake fuskanta.

Exit mobile version