Wakilinmu" />

Sai An Koma Salon Mulkin Magabatanmu Kasar Nan Za Ta Daidata – Alhaji Auwalu Isa Hassan

Ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara, gwamnatin tarayya ta ware don tunawa da ‘yan mazan jiya, mutanen da suka yi gwagwarmar sama wa kasar nan yancin kai wanda ya zo dai dai da lokacin da ake bikin murnar cikar kasar nan shekaru 50 da karewar yakin basasa, ba tare da kasar an sami baraka ko rashin jituwa a sakanin dimbin kabilun kasar nan da Allah ya albarkace ta da su ba.

Bisa ga haka, daya daga cikin masu kishin ganin kasar nan ta samu tsayawa da kafarta kamar sauran kasashen da suka samu yancin kansu suka tsayawa lokaci guda, Awwalu Isa Hassan, ya tofa albarkacin bakinsa a tattaunawar da ya yi da wakilimmu dake Jos fadar gwamnatin jihar Filato, a game da muhimmancin ranar.

Alhaji Hassan wanda shi ne shugaban ‘yan kasuwar Jihar Filato sashin masu sayar da kayan abinci a kasuwar Laranto Jos, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya ci gaba da rufe kan iyakokin kasar na tudu ya ce haka zai kara inganta tsaro da tattalin arzikin kasar nan, kuma ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa da walwatar arzikin kasar nan. Ga yadda hirar ta kasance.

 

Gwamnati ta ware ran shabiyar ga watan Janairu na kowane shekara ta zama ranar da ake adu’o’i, ga mazan jiya me za ka ce game da irin wannan ranar?

 

A gaskiya wadannan magabata sun yi aiki domin idan ka duba har gobe kasar nan tana tafiya ne bisa ginshikan da suka tsarawa kasar, mu dauka daga man fetur din nan da ita cen ginshikin tattalin arzikin kasar. Idan muka dubi irin ayyukan da suka kawo mana na ci gaba a kasar nan, za mu ga misalin bangaren ilmi da na kiwon lafiya, da manyan kamfanoni sadarwa da na yada labarai, kamar gidajen waya da gidajen radi’o, da kuma bangaren kasuwanci kamar masaku da kamfanin hada motoci na Kaduna. Haka nan kuma, sun gina ingantattun filayen jiragen sama da shimfida hanyoyin jiragen kasa, kuma sun jajirce kan habaka aikin gona wanda yake samar da mai shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar nan wanda kowa yasani da kudin da ake samu daga aikin gona a wannan lokacin aka sami hako mai wanda muka dogara akai a halin yanzu, da sauran muhimman abubuwa da suka aiwatar wadanda ba sa kirguwa kuma har

a gobe ake cin moriyarsu

To wane kira za ka yi ga al’ummar kasar nan?

A kullum na kan yi kira ga al’ummar kasar nan musamman matasammu da su rika nazari bisa kyawawan ayyukan da wadannan shugabanni suka gina da kuma gudanar da mulkinsu don su yi koyi da su domin idan ka duba su kishin kasa ne kawai suka sa a gaba ba gina kawunansu ba kamar yadda yawancin shugabannimmu na yanzu ke yi, domin idan ka duba da yawa daga cikin shugabannimmu da suka gabata za ka ga ba sa son tara dukiya da gina gidaje kamar yadda na yanzu ke yi domin wadansun ma har suka koma ga Allah ba su gidan kirki nasu na kansu kuma ba su bar kudade a banki ba, domin su a kullum burinsu kawai shi ne ya za a yi kasar nan ta samu ci gaba mai inganci.

Haka kuma sun gudanar da mulkinsu ba tare da suna nuna ban-bancin kabilanci ko addini kamar yadda muke gani a yanzu ba, domin dukkansu suna aiki a kan manufa daya don cimma burin na yaya kasar za ta sami cigaba.

Exit mobile version