Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Al’ummar Jihar Kano sai sun shafe Shekara 50 ana amfanar kyawawan ayyukan alhairin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam), jawabin haka ya fito daga bakin Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na Jihar Kano Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi alokacin da yake yiwa Jaridar Leadership Ayau karin haske kan nasarorin da Gwamnatin Ganduje ta cimma a wadannan shekaru biyar da ya yi akan karagar mulkin Jihar Kano.
Gogaggen Malamin Makarantar wanda kuma ya taba tsayawa takarar Sanata a Jihar Kano, kwamishinan ma’aikatar ayyuka na Jihar Kano Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi yace, duniya zata jima tana tunawa da tagomashin alhairin Gwamna Ganduje, musamman idan aka dubi yadda ake gudanar da ayyukan da ba’a taba samun wata Gwamnati data kamanta irinsu ba. Yace aikin kawata Jihar Kano domin shiga sahun manyan biranen duniya na daya daga cikin dubban ayyukan da ido ke iya gani hannu kuma ya taba a jihar Kano. Wadannan ayyuka sun hada da gadojin da wasu daga cikinsu sai a kasasjen turai ake ganin makamantansu, domin wanda duk ya hangi gada mai hawa uku wadda aka kammala aikinta a shataletalen Dangi zai aminta dani cewar tamu ba irin tasu bace.”
Unguwar Rimi yace al’amarin samarwa da matasa sana’un da zasu iya dogara da kansu ne ya sa Gwamna kirkirar wata cibiyar horar da sana’u iri daban daban da suka tasamma kala talatin wadda itima tuni an gama aikin tare da zuba kayan koyar da sana’u, harma an sa mata sunan hamshakin dan kasuwar nan dan asalin Jihar Kano Alhaji Aliko Dangote, wadda ke kan titin Zaria a Jihar Kano. Ga kuma aikin karasa manyan asibitocin da Gwamnatin baya suka yi watsi dasu, wanda ke kan titin zuwa gidan Zoo da kuma wanda ke unguwar Giginyu duk an kammala su harma sun fara aiki ka-in-da na’in.
Ya ci gaba da cewa Gwamna Ganduje ya taka rawar gani ta fuskar inganta harkar tsaro a Jihar Kano, domin wannan kokari nasa musamman dogaro da Allah da kuma rungumar harkokin addu’a yasa yanzu haka Jihar Kano ta zarta daukacin Jihohin kasarnan zaman lafiya, alhamdulillahi yanzu kowa sha’awar shigowa Jihar Kano yake yi domin gudanar da harkokin kasuwanci sakamakon kwanciyar hankalin da ake kwankwada.
A karshe Kwamishinan ya jinjinawa al’ummar Jihar Kano bisa goyon bayan da suke baiwa wannan Gwamnati, inda ya bukaci al’ummar da su kara jajircewa kan wannan kyakkyawar fahimta da suke nunawa Gwamna da Gwamatin Jihar Kano.