Connect with us

LABARAI

Sai Badi Daliban Nijeriya Za Su Rubuta Jarrabawar WAEC – Ministan Ilimi

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewa daliban da ke ajin karshe a matakin karama da babbar sakandare na kasar nan ba za su rubuta jarrabawar kammalawa ta WAEC ba da aka tsara gudanarwa nan gaba kadan.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayyana haka a jiya Laraba ga manema labarai na fadar gwamnati, jimkadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta gtarayya na wannan makon.

Ministan ya yi karin bayanin cewa, gwamma daliban kasar nan su maimaita shekarar karatu da a ingiza su hanyar kamuwa da cutar Korona.

Wakazalika, Ministan ya ce ga dukkan alamu ba za a bude makarantu nan kusa ba saboda kiyaye dalibai da malamai hadarin kamuwa da Korona.

Idan ba a manta ba dai, Kwamitin Yaki da Korona na Shugaban Kasa ya bayyana komawar daliban ajin karshe da za su rubuta jarrabawar kammalawa a matakin firame da sakandare makaranta; ranar 1 ga watan Yulin 2020, yayin da shugabansa, Boss Mustapha yake jawabi a kan matakin da shugaban kasa ya dauka game da sassauta dokar kulle, ranar Litinin 29 ga watan Yunin 2020.

Sai dai rahotanni sun nunar da cewa, dalibai da malamai duk sun ki hallara a makarantu walau na gwamnati ko masu zaman kansu a ranar da a ka ayyana, saboda tsoron kamuwa da Korona.
Advertisement

labarai