Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Sai Da Hujjar Ilimi Ake Tabbatar Da Yawaitar Mace-mace – Dakta Aminu Sulaiman

by Muhammad
December 30, 2020
in RIGAR 'YANCI
4 min read
Mace-macen
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mustapha Ibrahim Kano,

Babu wata hukuma ko cibiya ko wani mutum da zai iya cewa a yanzu ko wani lokaci da ya wuce an samu yawaitar mace-mace ko karancinsa, sai akwai kwakkwarar Hujja ta Ilimi da ya dogara da ita. Sannan za a iya yin bayani ya zama karbabbe ga masana a wanan fanni domin dai ilimi gaskiya ne kuma komai yana da maauni na ilimi ya zama karbabbe ga masana ako ina cikin duniya ba a shaci fadi ba, haka abin yake.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwararre akan harkar gwaje-gwaje da binciken jini dan gano lafiyar dan adam ko akasin haka, kuma Manajan Darakta sanna shugaban cibiyar binciken kulla da lafiyar al
umma ta ‘Klinche Lab Dig’, da ke Kano, Dakta Aminu Sulaiman, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke birnin Kano ranar Lahadin da ta gabata.
Har ila yau Dakta Aminu wanda ya bayanna cewa akwai lokacin da aka ce an samu yawaitar mace-mace a Kano musammam a lokacin da aka kulle garin da wasu Jahohi na Nijeriya yayin da aka samu barkewar Annobar Korona wacce ta zama alakakai ga duniya baki daya, a nan ne wasu suka yi ikirarin an samu yawaitar mace-mace a Kano.
To babu wata hujja ta ilimi da za ka bayar don tabatar da wannan bayani shin gaskiya ne ko akasin haka, domin a baya baka da alkaluma na yawan wadanda suke mutuwa a kullum wanda ake kira ‘Basic lane’ wadanda da su ne za ka iya gane cewa yau mutane kaza sun rasu, kumar dai kace yau biyu sun rasu gobe uku sun rasu, to tun da baka da wannan, baka da wannan alkaliman to ba ka da wata Hujja da zaka ce an samu yawaitar mutuwar a wannan lokaci musamam kamar abin da wasu masana su ka yi ikirari a wancen lokaci.
Haka kuma, a wancen lokacin fito da wani bayani shi ma mai rikitarwa inda wani ayari na hukumar yaki da cutar Korona (NCDC) ya zo Kano karkashin jagorancin Dakta Nasiru Sani Gwarzo, bayan da aka gwada mutum 10 masu alamarta, sai bayani ya fito cewa cikin mutum 10 din nan biyar zuwa shida har takwas suna dauke da ita, daga nan kuma sai aka ce mutanen Kano cikin mutum 10 takwas na da cutar, wanda ni kuma sai na kalli abin kamar wata siyasa ce ta shafawa Kano kashin kaji, domin sai ka yi wa mutum gwaji za ka ka gane yana da alamun cutar sannan a ba da bayani, amma da masu alamun cutar da marasa alamun cutar baka gwada su ba kuma ka ba da bayanin da babu tabbas? wannan shi ne abin tambaya.
Buku da kari Dakta Aminu Sulaiman ya kara da cewa ita kanta cutar Korona, ba za ka ce babu ita ko ta tafi ba sai ka gwada dukkanin mutane musamman masu alamun cutar sannan za ka ba da bayanin sakamakon, tunda za ka ga wani ma bai san yana da cutar ba wani kuma zai yi ta har ma ya warke bai sani ba, tun da yake babu wani takamaimai ko hakikanin maganinta kai tsaye da aka gano a halin yanzu, sai dai kawai a yi wasu ‘yan dabaru na masana cututtuka wato likitoci domin akwai kasashen da suka cigaba suna ganin ta tafi, amman daga baya ta dawo, su ma da suke da kayan gwaje-gwaje wadatattu ke nan ina ga mu Nijeriya ko Afirka baki daya.
Saboda haka shawarata ga al’umma ita ce, da zarar mutum ya ji wasu alamu a jikinsa to ya je cibiyar gwajin a gwada shi ko wacce irin cuta ba wai Korona kawai ba, domin ita kanta Korona din bai kamata mutum ya yi wasa da ita ba domin in ka kamu ba ka dauki mataki ba to matsala ce, domin za ka yada ta tsakanin iyalai ‘yan uwa da ab0kan aiki, makota ko abokan kasuwancin da sauran harkokin yau da kullum.
Wannan babar illa ce ko a ce ka samu kanka a wanda za a killace ai ba za ka ji dadi ba, kamar fa a ce ba ka yi laifi bane a kai ka gidan kurkuku, don haka akwai bukatar daukar matakan tabatar da lafiyarka ako da yaushe.
Dakta Aminu ya ce mu da muke da dangantaka biyu da ta shafi wanan cuta ta Korona na farko shi ne ta hanyar gwaji ake gane cutar to mu kuma a wuarin gwaji muke ko da yaushe, kuma abu na biyu gwajin shi ne aikinmu a matsayin hanyar rayuwa, don haka mun fuskanci kaluballe ta hanyar, sai da muka rufe wannan cibiya na sati guda zuwa sati biyu bisa shawarar hukumur kula da ma’aikatu da cibiyoyin lafiya, amma sai muka ga akwai bukatar mu bude mu cigaba da aikin gwaje-gwaje na masu cutar Suga, Hawan Jini, Taifot da sauran cututtukan da ke adabar al
umma, cikin taka tsan-tsan da daukar matakan yakar Korona don gudun kamuwa da ita ta wannan aiki namu.
A karshi dai ya yabawa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan daukar matakai na yakar Korona a Kano inda kuma ya shawarci alumma da su ba wa gwamnatoci da sauran hukumi da cibiyoyin kula da lafiya a hada kai domin yakar Korona da sauran cututtuka don tabatar da lafiyar alumma, inda ya bayyana manyan alamomin Korona su ne; ciwon makogwaro, mura mai zafi, kasala, ciwon kai, atishawa, sarkewar numfashi, da sauransu, don haka sai a kula da kai ta hanyar daukar matakai da kuma yin addu`a a matsayinmu na Musulmai.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Jami’an Lafiya 476 A Abuja Sun Kamu Da Korona, Inji FCTA

Next Post

Burina Farfado Da Tattalin Arzikin Karamar Hukumar Tarauni – Abubakar Zakari

RelatedPosts

Ingantaccen zabe

Aniyar Ganduje Ce Ta Haifar Da Ingantaccen Zabe A Kano – Yusif Ali

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana cewa, kyakkyawar aniyar Gwamna...

Kaduna

Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Kwanton Bauna A Kaduna

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Sojojin da ke karkashin ‘Operation Thunder...

Farar Hula

Hankula Sun Tashi A Maiduguri Bayan Babbaka Sojan Da Ya Harbi Farar Hula Hudu

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mutanen Maiduguri sun shiga tararrabi bayan...

Next Post
Tarauni

Burina Farfado Da Tattalin Arzikin Karamar Hukumar Tarauni – Abubakar Zakari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version