Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC), Malam Mele Kyari, ya bayyana cewa, sai da aka roki masu sayen man Nijeriya a kan su sayi danyen mai a kan Dala tara ga duk gangan mai a watan Afrilu.
Kasuwan main a duniya farashin mai ya sauka kasa wanda ta kai ana sayar da kowacce ganga a kan naira 15.98 a watan Afrilu, wannan shi ne karancin farashin da aka taba samu tun a shekarar 1999, hakan ya faru ne sakamakon fadan da ake tsakanin kasar Saudiyya da kasar Rasha.
“A zahirin gaskiya, mun sayar da kowacce gangan mai guda daya kan dala tara a watan Afrilu kuma sai da muka raki masu saya kafin suka saya a hakan,” in ji Kyari lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Ya kara da cewa, Nijeriya tana samar da mai ganga miliyan 2.49 a duk rana a watan Afriru, wanda aka ci tsammanin samun fitar da ganga miliyan uku a duk rana. Shugaban kamfanin ya ci gaba da bayyana cewa, wannan shi ne shekara mafi muni da kamfani da kuma tattalin arziki duniya ya fuskanta. Ya kara da cewa, yana da matukar mahimmanci kamfanin ya gudanar da wasu canje-canje.