Daga Alhussain Suleiman,
Sai da tsaro tattalin arzikin kasa ke bunkasa da kuma cigaba sannan ne zai baiwa al’umma dammar sakewa da kwanciyar hankali, har ila yau zai kuma baiwa yankasuwa dammar jin dadin gudanar da harkokihn sun a kasuwanci da kuma shigowar yankasuwa batare da fargaba ba. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Malam Hikimatullahy K. Yahaya alokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Malam Hikimatullah ya cigaba da cewa matukar tsaro suka inganta zai baiwa bakin yankasuwa dammar shigowa jihar Kano da sauran jihohin kasar nan tun da sun tabbatar cewa akwai natsuwa da kwanciyar hankali, domin har yanzu ana kara samun fuskantar matsalolin tsaro.
Da yake karin haske game da sabbin rundunonin sojojin kasar nan da aka canza Hikimatullah ya ce da yardara Allah kwalliya za ta biya kudin sabulu, tun da shugaban kasar ya amsa kiraye kirayen al’ummar kasa na canza manyan sojojin.Manajan daraktan na H K Y INTERGRATED CONCEPT da ke kasuwar Kofar wanbai a Kano ya ce al’umma su zura Ido matukar aka yi hakuri za’a ga canji akan harkokin tsaro a fadin kasar nan musamman inda aka fi samun masu tayar da kayan baya kamar masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa . Kiran da za mu ga shuganban kasa shi ne ya tabbatar ya ba kwarin gwiwa tare da wada ta su da kayan aiki irin na zamani, sannan shugaban kasa ya rika bibiyan abin da ke faruwa.
A matsayin shin a dankasuwa ya nab akin kokarin shi wajen samar da aiki mga wasu daga cikin matasan jihar Kano ba ya ga habaka tattalin arzikin jihar da na kasa baki daya. Saboda haka sai ya shawarci gwamnatin da ta rika taimakawa masu sana’ar kasuwancin Takalma, kamar yadda ake taimakawa sauran yankasuwa.Har ila yau yana da kyau gwamnan Kano ya rika tuntubar su domin bas u shawarwarin da suka kamata akan harkokin kasuwancin jihar domin su ba bu abin da suka sani sai harkokin kasuwanci.