Abubakar Abba" />

Sai Gwamnati Ta Zuba Jari Mai Yawa A Noma Za A Yaki Yunwa – Kwararru

Musa Malumfashi

kwarru a fannin aikin noma rani a kasar nan sun yi nuni da cewa, sai idan Gwamnatin Tarayya ta zuba jari mai dimbin yawa a fannin aikin noma sannan za iya iya yakar yunwa a shekarar 2021.

Manoman kwararru a Dam Gurara a garin babban birnin tarayyar Abuja ne suka bayyana hakan, inda kuma suka bukaci Gwamnatin Tarayya ta zuba jari mai yawa a fannin noma.
Manoman sunyi kiran ne a hirarsu da manema labarai, inda daya daga cikin manoman Dakta Samaila Aliyu mazunina a babban birnin tarayar Abuja, ya sanar da cewa, akwai bukatar gwamnatin ta yi dubi kan ayyukan manoman rani a kasar nan.
Ya kuma bukaci ma’aikatar aikin noma da raya karkara data yi hadaka da ma;aikar albarkatun ruwa wajen fadada noman rani a kasar nan, musamman a yankunan da akafi yin noman na rani.
Shi ma wani manomin Dakta Salisu Ahmed Gusua, wanda ya shafe shekarau 41 a fannin ya shawarci ngwamnatin ta kara mayar da hankaili wajen bunkasa fannin a daukacin kasar nan yadda maoman zasu yi noma mai yawan gaske.
Ya yi nuni da cewa, “ Mu na da Madatsun ruwa da dama a kasar nan da za’a iya yin amfani dasu wajen yin noman rani, amma abin taiakaici, ba a yin amfani dasu.”
Ya kara da cewa, akwai kuma ma’aikatar albararkatun ruwa ta tarayya,a amma abin takaici basa tura wani ruwa, hakan munyi zagaye a daukacin jihohin a Arewacin kasar nan, inda kuma daukacin su, ba su da wadatattun Madatsun ruwa.”
Ya sanar da cewa, manoman sun buge ne wajen sayen janartocin ban ruwan rani kuma ba sa samun wani sauki, musamman gannin yadda suke yawan sayen man fetur don zuba wa janartocin nasu don yin ban ruwa a gnakan su.
Ya kuma bukaci gwamnati ta samar da ingnataccen irin noma ga manoman da ke noman rani yadda za su dinga samu yin girbi mai yawa da kuma samar masu da hanyoyin yin rance daga bankuna don yin noma.
Shi ma wani manomin Adams Peter Eloyi dake a jihar Kaduna ya bukaci gwamnatin ta zuba jari mai yawa a fannin na noma, inda ya yi nuni da cewa, hakan zai kara taimakwa wajen rage rashin ayyukan yi a kasar nan zuwa kashi arba’in bisa dari.
Ya yi nuni da cewa, Nijeriya na barta a baya, amma idan gwamnati ta mayar da hankali wajen habaka fannin za a iya kairkiro da dimbin ayyukan yi da habaka tattalin arzikin kasar nan da kuma magance kwararowar wadanda suke a karkara zuwa cikin birane.
Shi ma Farafesa Daniel Gwary dake a sashen aikin noma na jami’ar Maiduguri ya sanar da cewa, akwai bukatar gwamnatin ta mayar da hankali kan yunkurin kasashe masu karfin tattalin arziki su 20 da ake son cimma a shekarar.
Ya yi nuni da cewa, za a iya cimma hakan wajen janyo matasa a jiki don su rungumi fannin na noma, inda kuma ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a a kakar bana a kara habaka fannin da kuma samar da wadataccen tsaro ga manoman a kasar nan.
Ya shawarci gwamnatin data kuma kawo karshen rikece-rikice a tsakanain manoma da Fulani mikiya da kuma yin garkuwa da manoman da ke kasar nan.
Ya kuma bayar da shawara da a kara ilimantar da manoma, musamman kananan manoma kan fasahar zamani ta yin noma domin su samu damar wadata kasar nan da abinci mai yawa da kuma kara karfafa noman rani.
Shi ma Shugaban kungiyar masu sarrafa Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim ya yi nuni da cewa, rufe iyakokin kan tudu da gwamnatin tarayya yi watannin baya, hakan ya kara taimaka wa fannin aikin noma a kasar nan.
A wata sabuwa kuwa, Gwamnatin Kebbi ta fara rabar da takin zamani na gwamnatin tarayya ga kimanin manoma 11,345 da annobar ambaliyar ruwa ta yi wa barna a shekarar 2018 a kananan hukumomi guda takwas a jihar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (SEMA) ce ta gudanar da rabar da kayan da suka hada da buhunhunan takin zamani mai guda 19,000 na samfarin NPK mai nauyin kilogiram 50 da kuma irin shinkafa da sauran su ga manoman su 2,000 da annbar ta ambaliyar rowan ta yi ta’adi a karamar hukumar Birnin Kebbi.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Alhaji Sani Dododo, wanda ya sanya ido a kan rabar da kayan ga manoman da abin ya shafa a karamar hukumar ta Birnin Kebbi a sakatariyar karamar hukumar a ranar talatar da ta gabata ya sanar da cewa, irin Rake da kudin say a kai naira miliyan 200 aka rabarwa da manoman Rake a dake a yankin Shanga cikin jihar.

Exit mobile version