Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Sai Kowa Ya Bayar Da Ta Sa Gudummawar Ne Za A Iya Dakile Shaye-Shaye –Alhaji Aliyu Yahaya

by Tayo Adelaja
September 18, 2017
in TATTAUNAWA
7 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Alhaji Aliyu Yahaya shi ne mataimakin babban kwamandan hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi na Jihar Kano, Atattaunawarsa da wakilinmu, Abdullahi Muhammad Sheka ya bayyana halin da aikin ke ciki sannan kuma ya warware zare da abawa kan kallon da ake yi wa hukumar. Mataimakin kwamandan ya kuma ya yaba kwarai da kokarin Gwamnatin Jihar kan yaki da shan miyagun kwayoyi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mai Karatu Zai so Sanin Wanene Alhaji Aliyu Yahaya.

samndaads

Alhamdu lillahi, ni sunana Aliyu Yahaya Mataimakin babban kwamandan hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Shin ko domin wadanne ayyuka aka samar da wannan hukuma dominsu?

Ranka ya dade batun shaye-shayen miyagun kwayoyin a halin yanzu ya zama tamkar ruwan dare, wanda kuma ke neman zame wa hukumomi kadangaren bakin tulu duk da kokarin da jami’anku ke yi ba dare ba rana, shin ko a ina gizo ke sakar?

A hakikanin gaskiya wannan mummunan sana’a wasu na kallon sana’a ce mai kawo makudan kudade wadda a zaton hanya ce mai bullewa, kuma ko kadan maganar ba haka ta ke ba, kwadayin samun kudi a huce ya sa wasu ke shiga cikin harkar. Duk namijin kokarin da jami’an wannan hukuma ke yi na kamewa tare da gurfanar da wadanda muka kama gaban kulliya, amma har yanzu wasu na ganin irin wannan hanya ya kamata su bi domin dogaro da ita. A hakikanin gaskiya wannan ba hanya ce mai dorewa ba, abubuwa ne da suka saba dokokin kasa da ma na addini, domin ba wani addini da ya amince da shaye -shayen miyagun kwayoyi.

Ranka ya dade kana magana a kan masu shan kwayoyin, su kuma masu fataucin nasu fa?

Ga su masu fataucin kwayoyin yawancin wadanda muke kamawa fada mana suke abokai ne suka jefa cikin wannan mummunar sana’a, ko damuwa ko rashin wata sana’a da ya kamata mutun ya dogara da ita, ka ga wannan ba dalili ba ne da zai sa mutun shiga wannan halin, dole ne ka yi abota da wanda ka tabbatar da munin sana’ar da yake? Kamata ya yi ka yi abota da wanda aka tabbatar da sahihancin hankalinsa da kyan dabi’unsa wanda zai amfani rayuwarka da addininka. Wasu kuma wai saboda rashin aikin yi ya sa suke wannan shaye -shaye, to ai neman aiki shi ya fi dacewa da shan kwaya, idan aka tabbatar da kana shaye -shaye wane zai dauke ka aikin?

A irin wannan batu, kenan akwai gazawar tarbiyya ko kulawa daga bangaren iyaye ko ita kanta gwamnati?

Akwai matsaloli da dama wanda duk Allah ya jibinta wa al’amarin wasu al’umma kamata ya yi ya dauki matakan da suka kamata na taimaka wa wadanda Allah ya damka ma amanarsu a hannunka, musamman yadda wasu masu wannan shaye -shaye ke nuna cewa rashin aikin yi ne. To, idan iyaye za su mai da hankali wajen koyar da sana’u da kuma lura da tarbiyar yaransu, idan gwamnatoci za su tsaya sosai wajen bude massana’antu za a samu saukin matsalar, wannan ta sa ako da yaushe muke jan hankalin gwamnatoci da iyayen yara wajen samar da sana’a ga al’umma.

Ganin yadda ake ta fama ana toshe can suna bude nan, shin ko akwai wasu sabbin dabaru ko matakai da wannan hukuma ke dauka domin ganin an dakile wannan bakar ta’ada?

Alhamdu lillahi, kwalliya na biyan sabulu domin har ofis din nan kungiyoyi ke zuwa domin neman yadda za a hada kai domin taimaka wa wannan aiki. Haka kuma muna gabatar da tarukan kara wa juna sani a kafafen yada labarai domin jawo hankalin jama’a wajen fahimtar matsalar da ke tattare da shaye -shayen kwayoyi da fatauncinsu.

Babban abin da jama’a suka kasa fahimta shi ne yadda jami’an wannan hukuma ke aiki ba dare ba rana, amma idan an toshe can sai nan ta bude, sai ka ji idan an tarwatsa sansaninsu na wuri kaza, sai ka ji sun koma wuri kaza, menene hakikanin matsalar?

A hakikanin gaskiya lamarin shaye- shaye lamari ne mai fadin gaske. Yanzu haka har wani kwamiti gwamnatin Jihar Kano ta kafa wanda aka hada jami’an tsaro daban-daban, kasancewar duk wurin da muka samu rahoto mukan tunkari wurin, musamman wani lungun baya shiguwa sai an shirya kwarai da gaske, sannan kuma Allah ya albarkaci Jihar Kano da Kwamandan wannan hukuma jajirtacce ne kwarai da gaske, ba shida tsoro ko shakka yana aikinsa bilhakki da gaskiya, ya sa muke aikin tunkarar ire-iren wadannan wurare domin gudanar da kame, masu shaye -shaye a yi masu nasiha wadanda muka kama da laifin sayar da kayan mayen mukan yi masu nasiha wadanda kuma za mu gurfanar da su gaban kulliya mu gurfanar da su. To idan mun kai irin wannan samame wadanda ba mu sami sa’ar kama su ba, sun gudu daga baya sai su tattara kansu su koma wani bangaren kuma, wannan ta sa muke kiran al’umma cewa a duk lokacin da suka ga ire-iren wadanann gungun masu shaye -shaye su gaggauta sanar da wannan hukuma domin daukar matakin da ya kamata.

Jama’a na tsoron bayar da irin wannan labarin masu aikata wasu laifuka domin gudun kar kuma wadannan bata gari su sani cewa wane ne ya sanar da jami’an tsaro labarinsu, shin ko wane tanadi hukumarka ta yi kan wannan matsala?

Kwarai kuwa duk lokacin da muka ba da irin wannan sanarwa mu kan tabbatarwa da duk wanda ya taimakawa jami’an tsaro da wani labari cewa ba abin da zai faru da su, kuma ko a kotu ba a tambayarmu inda muka samu labari, ka ga kuwa tun da kotu ma ba za ta bukaci inda muka samu labarin ba, saboda haka wannan sirrinmu ne ba wanda zai san wanda ya sanar da mu. Saboda muke tabbatarwa da al’umma cewa kar su ji komai, akwai sirri tsakaninmu da masu ba mu labarai, sannan kuma lura da lafiyarsu na cikin abubuwan da suke da muhimmanci a wurinmu.

Ka yi maganar wata hadakar jami’an tsaro da gwamnati ta samar don tunkarar wannan aiki, shin akwai wani taimako da kuke samu don cin nasarar aikin?

Alhamdu lillahi wannan gangamin jami’an tsaro gwamnatin Jihar Kano ce ta kafa ta domin kishin al’ummarta, ta yi haka domin tabbatar da al’umma ingantacciya mai cike da tarbiyya mai kyau, wannan ta sa aka samar da wannan gangami na jami’an tsaro wanda kwamandan Hukumar yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi ke shugabanta.

 

Cikin rukunonin masu mu’amula da miyagun kwayoyi, daga kan masu fatauci zuwa kan masu shan kwayoyin, shin ko akwai wani dacen kame wasu hamshakan diloli da hukumarka ta yi?

Kwarai da gaske mun yi nasarar damke wasu gagararru da suka addabi wasu unguwannin cikin Birnin Kano, ina tabbatar maka da cewa akwai wadanda muka kama wadanda manyan masu laifuka ne da ma’aikata ke nemansu ruwa a jallo, mun gurfanar da su gaban kulliya yanzu haka da yawansu suna gidan sarka.

Wasu na kokawa kan yadda idan kun kama wasu dilolin kwayar kwanaki kadan sai a gansu sun dawo sun ci gaba da sana’arsu?

Haka kuma yanzu haka a cibiyar Nasiha da koyar da sana’a ga wadanda muka yi wa irin wannan horo da ake ginawa, amma tuni aikin ya tsaya, muna kara mika godiya ga Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu wanda har wakilinsa ya turo domin duba inda aikin ya tsaya don ganin yadda za a kara sa shi, idan muka samu kammala wannan aiki ko shakka babu za mu samu sukunin ci gaba da gudanar harkar nasiha da kuma koyar da sana’u, idan ma Allah ya ba mu iko mu samar da wani tallafi domin ganin wadanda suka samu wannan horo ba su koma gidan jiya ba.

Suma jami’an wanan hukuma muna mika godiya kwarai da gaske bisa jajircewar da suke wajen ganin an kawo karshen wannan matsala ta shaye -shaye a jihar Kano, sai kuma shi kansa babban kwamandan hukumar wanda yake bayar da dukkan hadin kai da kuma karfin guiwar aiwatar da ayyukan wannan hukuma, muna fatan Allah ya kara masa lafiya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Katsina Za Ta Gina Kwalejin Horon Sana’o’i A Garin Majigiri

Next Post

Ba Abin Da Ya Kai Zaman Lafiya Dadi A Duniya —Sanata Matori

RelatedPosts

Shugaban RIFAN

Kowa Ya Ci Bashin Noma Sai Ya Biya – Shugaban RIFAN Na Kano   

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa na Kasa  (RIFAN) reshen Jihar Kano,...

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

HON. MUHAMMAD UBA GURJIYA MAI SHANU shine wakilin al'ummar karamar...

Gwamnatin Jihar Kano Tana Bukatar Kowa, Inji Ibrahim Usman Bala

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Haruna Akarada, A ci gaban da gwamnatoci ke kokarin...

Next Post

Ba Abin Da Ya Kai Zaman Lafiya Dadi A Duniya —Sanata Matori

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version