Connect with us

LABARAI

Sai Me Don Na Saya Wa Matata Wayar Naira 400,000 – Kwamishinan Neja

Published

on

Sakamakon rade-radin da ke ta yawo musamman a kafafen yada labarai na yanar gizo wanda ke nuni da cewa Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu a Jihar Neja, Alhaji Abdulmalik Sarkin Daji, ya yi wa matarsa kyautar wayar iPhone 11 Pro, a ranar bikin taya ta murnar ranar haihuwarta, Kwamishinan ya kunyata masu sukar sa a kan hakan da cewa, “ai Ina da halin saya wa matata wayar ma da ta fi haka tsada.”
Da ya ke zantawa da wakilinmu a bayan bayyanar rade-radin da suka biyo bayan bayyanar faifan bidiyon, Daji cewa ya yi, sam bayar da kyautar wayar  iPhone ta naira 400,000 ga matana a lokacin da take bukin murnar ranar haihuwarta, bai kamata ya zama wani abin surutu a kansa ba, ya kara da cewa, tabbas ta ma cancanci sama da hakan.
Sai ya musanta zargin cewa an shirya kasaitaccen buki ne a wajen, inda ya ce an yi bukin ne a tsakanin iyalan gidansa kadai a dakin cin abincinsu.
Ya bayyana cewa a matsayinsa na kwararren Lauya, kuma wanda ya riki mukamin shugaban karamar hukuma har karo biyu, bai kamata ya zama abin surutu ba in ya saya wa matarsa wayar ta iPhone 11 a ranar bukin murnar ranar haihuwar nata a matsayin kyauta, domin yana da karfin yin fiye ma da hakan.
“Har motoci mutane sukan siya wa matansu a lokuta irin wannan, to me ya sanya ake suka ta don ni na saya wa matana wayar hannu. Masu suka ta so kawai suke su zubar mani da kima saboda kasancewata Kwamishina.
Kwamishinan ya ce, shi bai ma san ko wace irin waya ce ba har sai lokacin da ya karanta labaran masu sukar nasa. Sannan ya kara da cewa, wayar ma kyauta ce daya daga cikin bankunan da ma’aikatarsa ke hulda da su ta yi masa.
“Ni ban ma san ko wace irin waya ce ba. A lokacin da aka yi mani kyautar ta wajen bukin murnar zagayowar ranar haihuwata, sai na yanke shawarar na ajiye ta har lokacin bukin murnar zagayowar ranar haihuwar matata na yi mata kyautar ta, musamman domin ganin da na yi ta nuna sha’awarta a kan wayar.
“Hakan ne kuma nakan yi a kowace shekara ga dukkanin matana da ‘ya’yana ko kafin ma na zama Kwamishina. Nakan ba su mamaki da kyautuka domin na nuna masu damuwa ta da su, don haka ina mamakin yanda wannan ya zama abin tsegumi a kafafen yada labarai na yanar gizo.
Kwamishinan ya ce yana da kudurin ya bai wa Uwargidansa kyautar ma da ta fi wannan a lokacin nata bukin murnar ranar haihuwar wanda za a yi nan ba da jimawa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: