Sai A Shekarar 2020 Nijeriya Za Ta Fita Daga Matsin Tattalin Arziki –Udoma

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Kasar Nijeriya zata fita ne dungurungun da matsalin tattalin arzikin kasa a shekarar 2020.

Furucn hakan ya fito ne daga bakin Mnistan Kasafin Kudi ta tsare-tsaren kasa Sanata  Udoma Udo Udoma.

Udoma ya bada wananan tabbacin ne a jawabin sa a  a taron masu ruwa da taski da cibiyar bnciken tattalin arzkin  kasa wato   (NISER), ta gudanar a garin  Ibadan cikin jihar   Ogun.

Ya ce, har yanzu akan matsalin tattalin arzikin kasa da Nijeriya ke fuskanta ba ta sake zani ba, kamar yadda, alummar kasar  suke ta maganar cewar kasar ta fita, sakamakon rahoton da  a kwanan baya Hukumar Kididdiga ta kasa ta sanar a kwanan baya.

A cewar Ministan, rahoton hukumar, kalubale ne kawai ga ‘yan kasa don su kara jan damara don ganin  kasar ta cimma burin ta samar da kasha bakwai na habaka tattalin arzikin ta kafin shekarar 2020.

Ya shawarci ‘yan kasar nan akan kada su yi kasa a gwaiwa wajen bada hadin kai akan yunkurin gwamnatin tarayya na sake wa tattalin arzikin kasar sabon fasali a kan kar kashin shirin gwamnatin tarayya na farfado da tattalin arzikin kasa.

Minstan ya ce, koda yake, gwamnati ta kiyasta cewar kasar nan zata fita daga kangin matsin na tattalin arzikin kasa a tsakiyar shekarar 2017, rahoton da hukumar ta kididdiga ta kasa ya fitar, ya baiwa gwamnatin kwarin gwiwa ne.

Ya kara tabbatar da kudirin gwamnti na kokarin dawo da martabar tattalin arzikin kasar nan musamman daga matsalar da aka samu a. Shekarar 2016, yadda za a samar da kashi bakwai bisa dari a shekarar 2020.

Ya yi kira ga ‘yan kasar nan dasu hada kai da gwamnatin ytarayya ta hanyar zuba jarin su akan ababen da zasu bunkasa rayuwar ‘yan kasa’inda hakan zai samar da aikin ga dinbin ‘yan kasar nan musamman matsa marasa aikin yi.

Ya kuma ja hankalin cibiyar da a koda yaushe ta kirkiro ilimi mai dorewa ta hanyar gudanar da bincike da koyar da horar wa da zasu taimaka wajen ciyar da kasa gaba.

Udoma ya ce, cibiyar nada babbar rawa da zata taka wajen tabbatar da shirin gwamnatin tarayya na farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Daga karshe ya yi kira ga mahukuntan cibiyar dasu kirkiro da sababbin tsare-tsare da gudanar da bincike da yin hadin gwaiwa da cibiyoyi ma su manufa irin tasu da ke kasar nan da kuma wadanda ke kasashen ketare don cimma burin gwamnatin tarayya na sanya tattalin arzikin kasar a kan turba mai dorewa.

Shi kuwa Darakta Janar na cibiyar, Dakta Folarin Gbadebo-Smith a nashi jawabn ya bayyana cewa, manufar tar bitar itace don a tattauna akan bangarorin tattalin arziki ma su sarkakiya da kuma nufin samar da mafita.

 

Exit mobile version