Abba Ibrahim Wada" />

Sai Watan Disamba Pogba Zai Dawo Filin Wasa, Cewar Solkjaer

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa dan wasan tsakiyar kungiyar bazai dawo domin cigaba da bugawa kungiyar wasa ba har sai watan Disamba mai zuwa.

Rabon da Pogba ya yiwa Manchester United wasa tun ranar 30 ga watan Satumbar daya gabata a wasan da kungiyar ta buga da Arsenal inda suka tashi 1-1 sai dai Solkjaer, bayan an tashi daga wasan da kungiyar ta samu nasara daci 3-1 akan Norwich City, ya bayyana cewa Pogba yana bukatar makonni biyar ne kafin ya warke.

Pogba wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da kwasar Faransa ya kasance jigo a tafiyar kungiyar duk da cewa a kwanakin baya yaso komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Sipaniya.

“Bana tunanin zamu iya ganin Pogba nan kusa sai dai a watan Disamba saboda yana bukatar ya huta sosai sannan kuma yana bukatar ya warke yadda yakamata domin ya dawo cikin koshin lafiya kamar yadda yake a baya” in ji Solkjaer

Ya cigaba da cewa “Babban burinmu shine kowanne dan wasa ya kasance cikin koshin lafiya saboda haka ina zaton zai iya dawowa a wasan da zamu fafata da kungiyar kwallon kafa ta Sheffield United a ranar 24 ga watan Nuwamba ko kuma bayan anyi hutun sati daya”

Sai dai har yanzu mutane da dama basu fahimci inda Pogba yaji ciwon ba saboda anga tafin kafar dan wasan a rufe tad a Bandeji sannan kuma shi Solkjaer ya bayyana cewa idon sahun dan wasan ne yake da matsala

Exit mobile version