Bilkisu Yusuf Ali" />

Sa’idu Faru: Gwarzonmu Na Mako

Tarihin Makada Sa’idu Faru:

Makada Sa’idu Faru yana cikin makadan a suka yi shura a kasar Hausa inda amon kidansu na kotso wanda ya yi zagaya a bangaren fada tarihi ba zai taba shafe shi ba.  Makada sa’idu Faru makadin Kotso ne da aka yi a garin Faru da ke masarautar Muradun da ke jahar Zamfara. An haifi Alhaji Sa’idu faru a shekarar 1916 mahaifinsa shi ne makada Abubakar Mai kotso . Shi Abubakar Mai kotso makadin fada ne har ya bar kida. Don haka shi kida gadonsa ya yi  shi kansa mahaifin sa’idu Farun ya gaji kida daga mahaifinsa wato kakan Sa’idu Fau  makada Alu mai kurya. Asalinsu Gobirawa ne, wato mutanen sabon garin Gobir. Shi Alu mai kurya makadin yaki ne shi yake yi wa sarakunan Gobir kidi lokacin da ana yaki. A sheakarar 1942 Sa’idu Faru ya dau gabaren gidan a kida suka dakatar da mahaifinsu saboda tsufa. Wanda Sa’idu Faru ya fara yi wa waka shi ne dagacin kauyensu Sarkin yamman Faru Alhaji Ibrahim a 1942. Mahaifiyarsa mutuniyar garin Banga ce a can cikin kasar Kauran namoda a jahar Zamfara. Sarkin yakin Banga Saleh Abubakar shi ne maigidan Sa’idu Faru na farko a rayuwarsa ta waka. Makada Sa’iu Faru ya shiga fagen kidan fada ne kamar mahaifinsa,  da shi ya fara, da kuma shi ya gama. Don haka ma yake yi wa kansa kirari a wata waka da ya yi wa marigayi galaiman Kano Alhaji Tijjani Hashim ina yake cewa

 

Jagora: Sa’idu Faru ka wakar mulki,

:Don haka komai ka jiya karya akai.

 

Daga baya uban kasa Hakimin Kauran namoda ya kwace Sa’idu Faru Alhaji Abubakar Garba wanda aka nada 1952. Sakamakon wakokinsa da ya ji wanda ya yi wa dagaci sarkin yaki Saleh. Don haka ya nemi yana son Sa’idu Faru ya dawo Kaura ya ci gaba da yi masa waka.

Daga cikin wakar da Alhaji Sa’idu Faru ya yi wa Uban kasa /hakimin gundumar kauran namoda Alhaji Aubakar Garba akwai:-

 

G/Waka: Gwabron Giwa na shamaki baba uban gandu,

:Abu gogarman Magaji mai kansakalin daga.

 

Jagora:Tun radda kayyi sarauta na madawaki kasagga tai haske,

‘Y/amshi: ko alkaryar kasam masar ba ta dara Kaura ba.

 

A shekarar 1953. Sarkin Zamfaran Zurmi  Sule  wato Uban kasar Zurmi wanda aka nada shi. Duk da yana da nashi makadin amma kalmomi irin na Sa’idu Faru sai ya nemi Sa’idu Faru ya yi masa waka. Don haka yana Kaura yana Zurmi.  Sarkin Kudun Maccido ma ya zamo ubangidan Alhaji Sa’idu Faru lokacin da aka kawo shi sarkin Kudu a shekarar 1953-1956 ya yi hakimci a garin Talatar Mafara. Ya kuma yi sarkin musulmi Allah ya jikansa da gafara amin. Duk da su Mafara suna da nasu makadi  Ibrahim Gursu amma  lokacin yana hakimi ko uban kasa   shauki ya kama shi shi da Muhammadu maccido sai ya yi wa Muhammadu Maccido kidi . Alhaji Sa’idu Faru kenan yana Banga yana Kaura yana Zurmi ga kuma  mafara ta samu saboda  dan sarkin musulmi da aka kawo.

Inda a wakarsa ya na cewa,

 

Jagora: Mamman dalilinka na san Talata

:Mamman dalilinka na zamni Hausa.

:Sarkin Kudu Maccido ci maraya.

 

Bayan da aka mayar da sarkin Kudu Maccido Sakkwato da aiki kafin ya zamo sarkin musulmi sai kuma Sa’idu faru ya yi wa sarkin Gabas na Mafara waka shi kuma dan gidan Bauren Dange Muhammadu ne da malama Usman wanda ya haifi sarkin musulmi Abubakar da wanda ya haifi sarkin kudu maccido duk zuriyarsu guda duk ‘yan gidan sarkin musulmi Mu’azu ne. Shi kuma dan dan sarkin musulmi muhammadu Bello ne sarkin musulmi muhammadu Bello dan Shehu Usmanu Danfodiyo. Zuriyarsu guda. A shekarar 1958 sai aka kawo shi talatar mafara . Sa’’idu Faru ya ci gaba da shi a matsayin maigida. A tsakani akwai sarkin Zamfara Aliyu  amma shi Alhaji Sa’idu Faru bai yi masa waka ba sai da aka kawo Sarkin Gabas Shehu sai ya rike shi a matsayin maigida.

Jagora: Sarkin Gabas Shehu Dan Bubakar,

’Y/amshi: Ci fansa uban jarimai.

Jagora: Ya kwashe martabar Bubakar

Y/Amshi: Ya bar wasu can na hauka.

 

Sarkin musulmi Abubakar na uku ya samu wakoki da dama wajen Sa’idu Faru inda yake nuna muhimmancin gidansu (Gidan mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo)  da tsarin muslunci na Najeriya don akwai inda yake cewa a wakarsa

 

Jagora: Shugaban musulmin Najeriya

Bubakar na Amadu baban Galadima

Allah ya ba ka albarkar Bubakar dan Bello.

 

Hikimomi da ya yi ta amfani da su a wakarsa suna fitowa da gidan mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo ne, tunda shi daga Sakkwato ya fito don haka a kara sanin muhimmancin wannan gidan na mujaddadi.

Yadda yanayin rayuwar Makada Sa’idu Faru take  akasarin rayuwar kidansa ya kare ne ne a tsohuwar lardin Sakkwato wato Zamfara da Sakkwato da Kabi a halin yanzu. Sannan abin da zai kara bayar da mamaki akasarin wakokinshi duk sun yi tasiri sun yi fice amma kuma akasarin wadanda ya yi wa wakar dagatai ne da Hakimai.  Za ka ji waka ta kai waka ta fada komai akwai ciki na tubalan ginin wakar fada amma sai ka ga hakimin kauye ne ko dagacin kauye. Daga baya ya dinga fita waje inda ya je Zariya  ya yi wa sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris waka sannan ya yi wa sarkin Yawuri marigayi Alhaji Tukur Abdullahi  waka ya yi wa  marigayi ‘Yandakan Katsina hakimin Dutsin-ma waka Alhaji Balan Goggo don shi ma ya zauna da Alhaji Sa’idu Faru zama na amana zama na mutunci. Sa’idu Faru yakan tafi Dutsin-ma a yi rangadi da shi a je zagayen kasa da shi don haka shi ma ana sanya shi a cikin iyayen gidansa A Kano ma ya yi ubangida marigayi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim ya yi maigida marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero anan ne ma ya yi waka guda ta mace wadda ita ce wakar da yi wa mace a iya yadda nazari ya kai wadda ya yi wa mai babban daki mahaifiyar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Inda yake cewa:-

 

G/Waka: Mai babban dakin kasar Kano

:Alhajiya babar Sa’idu

 

Jagora: Uwar Turaki uwar Dan’isa

‘Y/amshi: Uwar Turaki Uwar Dan’isa

 

Jagora: Uwar Turaki Uwar Dan’isa

’Y/amshi: Uwar Sarkin waka Sa’idu

 

Jagora: Ba ta yarda da wargi ba

’Y/amshi: Tana shire ‘yar malam muhamman

Jagora: Idan Allah yacce ka samu,

’Y/amshi: Kowa ba shi hana ka samu

Jagora: In Allah yab baka ka samu

’Y/amshi: Ka lura ka zan godewa Allah

Jagora: In Allah bai ba ka samu ba

’Y/amshi: Lura ka zan Allah guda na

 

Alhaji Saidu Faru ya yi shekara 71 a duniya. Ya rasu a shekarar 1987 ya bar ‘ya’ya goma sha biyu maza shida mata shida  da matan aure biyu. Kaninsa Mu’azu wanda shi ne kamar Daudun kidi duk da shi  Mu’azun Allah bai yi masa tsahon rai ba. Sai dansa na cikinsa Alhaji Ibrahim wanda shi tsohon ma’aikacin hukumar dansa ne wanda da ma tun yana yaro yana amsawa a cikin wakar za a ji inda shi Sa’idu Farun yana yi masa godiya. Shi ya dau gabacin gidana  a shekarar 1989 wanda shi ne ke jagorancin gidan har yanzu.

 

An samu wannan bayani daga bakin shahararren manazarci kuma masanin tarihin makadan baka na gargajiya Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin magaji Daga Jahar Zamfara Najeriya.

Exit mobile version