Sa’in Jama’a Ya Bukaci Al’umma Da Su Rungumi Sakamakon Zabe Cikin Natsuwa

An bukaci al’umma karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna dama Nijeriya gaba daya da su kasance a natse tare da bin doka da oda a yayin da aka sanar da sakamakon zabe, don kaucewa barkewar rkici kamar yaddda aka samu a lokuttan baya, musamman abin da ya faru a shekarar 2015 wannnan shawarartya fito ne daga bakin Tsohon Shugaban Karamar hukumar Sabon Gari kuma tsohon dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Alhaji Ya’u Usman, Sa’in Jama’a, a yayin da yake tattaunawa da wakilinmu bayan ya kada kuri’arsa a zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu 2019.
Ya kuma yi kira ga hukumar zabe ta INEC da ta tabbatar da ta gudabar da sahihin zabe, wanda zai samu karbuwa ga dukkan jami’iyyun siyasa, “Hakan zai kara mutumci shugaban hukumar zaben, musamman ganin wannan ne zaben gama gari na farko da zai gudanar a fadin kasar nan tun da ya karbi ragamar shugabancin hukumar’” inji shi.
Daga nan ya kuma yi korafin cewa, a wasu wurare an samu rahoton musgunawa ‘yan jam’iyyun adawa wanda hakan babbar karya dokar zabe ne, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kasance a ‘yan ba ruwan mu a harkokin zabe, kada kuma su yarda a yi amfani da su wajen takurawa ‘yan adawa a sauran zabukkan dake tafe.

Exit mobile version