Connect with us

WASANNI

Saka Riga Mai Lamba 7 Ba Karamin Girma Ba Ne A Real Madrid

Published

on

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Mariano Diaz, ya bayyana cewa saka riga mai lamba 7 a kungiyar ba karamin girma bane duba da yadda wadanda suka saka lambar kafin zuwansa.

Kungiyar kallon kafa ta Real Madrid dai ta bawa Diaz riga mai lamba 7 ne bayan ta siyoshi daga kungiyar kwallon  kwallon kafa ta Lyon dake kasar Faransa bayan tashin dan wasa Cristiano Ronaldo zuwa Jubentus.

Sai dai tun bayan komawar dan wasa Diaz Real Madrid rahotanni suka bayyana cewa kociyan kungiyar da shugabannin kungiyar suna fatan dan wasan zai maye musu gurbin Ronaldo wanda ya jefa kwallaye 450 cikin wasanni 438 a kungiyar.

“Saka riga mai lamba 7 a Real Madrid ba karamin aiki bane saboda kowa yana ganin tunda kana saka rigar dole sai kayi kokari kuma kaima kana bukatar hakan ganin wadanda suka saka rigar a baya wato Ronaldo da Raul sun kafa babban tarihi a kungiyar” in ji Mariano

Ya ci gaba da cewa “yanzu aikin da yake gabana shine inga na bawa marada kunya ta hanyar cin kwallaye masu yawa sannan kuma in taimakawa kungiyar ta kowacce hanya domin ganin mun samu nasara”

Mariano dai ya zura kwallo a raga a wasan da Real Madrid ta doke kungiyar Roma daci 3-0 a gasar cin kofin zakarun turai kuma shine ya zura kwallo ta uku bayan ya shigo wasan a minti na 73 da fara wasa.

 
Advertisement

labarai