Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya bayyana cewar sakamakon gwaje-gwajen da aka yi masa kan cutar Korona ya nuna bai kamu da cutar ba.
Tambuwal wanda ya killace kansa a ranar Juma’ar da ta gabata a dalilin hulda da wasu muhimman mutane wadanda suka kamu da cutar ya ce a yayin da ya killace kansa ya gudanar da nau’ukan gwaje-gwaje daban-daban kamar yadda yake a ka’idar kiyaye kamuwa da Korona.
“A cike da godiya ga Allah madaukakin Sarki nake sanar da al’umma musamman na Jihar Sakkwato cewar sakamakon gwaje-gwajen da na yi sun tabbatar ban kamu da wannan cutar ba.” In ji Gwamnan a bayanin da ya sanyawa hannu da kansa a daren jiya.
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Jihar da su ci-gaba da bayar da goyon baya ga jajirtaccen aikin da Hukumomin da ke bayar da kariya kan cutar Korona a ciki da wajen jiha ke yi ta hanyar bin dukkanin ka’idoji da sharuddan kiyaye yada cutar.