Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Sakamakon Gwaji Ya Nuna Shugaban NIS Ya Kamu Da COVID-19

A matsayinsa na daya daga cikin shugabannin manyan hukumomin gwamnati, Shugaban NIS ya nuna kishin kasa game da yaki da cutar COVID-19 ta hanyar mika kansa da kansa a yi masa gwaje-gwaje bayan dawowarsa daga Ingila.

Tun daga ranar da ya dawo, 22 ga watan nan na Maris, Babandede ya kebe kansa kamar yadda gwamnatin kasa ta umurci duk wani dan kasa nagari da ya dawo tafiya daga waje ya yi.

Bayan kammala gwaje-gwajen da aka yi masa, sakamakon ya bayyana cewa shugaban ya kamu da cutar ta COVID-19, sai dai babu wata damuwa sosai kasancewar jikinsa da sauki kuma maganin da ake masa ana samun dace a kai.

A wani takaitaccen sako da Shugaban na NIS, Muhammad Babandede ya aika wa wakilinmu ya yi kira ga masoya da ‘yan’uwa da abokan arziki da daukacin jami’an NIS su taya shi da sauran dukkan ‘Yan Nijeriya da suka kamu da cutar ta COVID-19 addu’ar samun waraka daga Ubangiji Mahalicci.

Haka nan ya nemi Jami’an NIS su ci gaba da zage damtse a kan ayyukansu tare da ba da goyon baya ga mataimakinsa mai kula da al’amuran gudanarwa domin hukumar ta samu damar sauke nauyin da kasa ta dora mata.

A halin da ake ciki kuma, Sanarwar manema labarai da Jami’in yada labaran NIS, DCI Sunday James ya fitar ta bayyana cewa Shugaban na NIS, Muhammad Babandede yana cikin kuzari kuma yana bayar da umurni game da ayyukan hukumar ta sashen intanet.

Sanarwar ta ce NIS za ta tabbatar da ci gaba da ayyukanta kamar yadda ya kamata duk da halin da ake ciki na jarabta a kasar nan, yayin da a hannu daya kuma ake ci gaba da addu’ar Ubangiji ya dubi bayinsa da idon rahama ya dauke wannan annoba daga doron kasa bakidaya.

 

 

Exit mobile version