Connect with us

DUNIYAR MAKARANTU

Sakamakon Rufe Makarantu (I)

Published

on

A yau shafin Duniyar Makarantu ya yi duba ne bisa yadda aka kulle makarantu sakamakon bullar cutar Korona, wanda hakan ya sa wasu makarantun suka koma ga yin nasu karatun ta ‘Online’ hakan ba karamin ci gaba bane. Dalilin faruwar hakan ne kuma wasu daliban suke ganin sun koma baya da karatunsu, wasu kuma suke ganin kamar hanya ce ta dakushewar karatun nasu gaba daya, saboda a yanzu ma sun fara mantawa da karatun da akai musu a baya. Cewarsu sun manta da karatun baya, ina kuma ga an ci gaba a hakan, wasu daliban kuma suna ganin hakan da a kai daidai ne sai dai kuma ya kamata a lalubo wata hanyar, amma ba wannan ba. Wannan shafi na Duniyar Makarantu ya zanta da wasu daga cikin daliban manyan makarantu inda suka bayyana nasu ra’ayin game da wannan batun, ga kuma yadda ta kasance:

Fatima Abdulrahman Abdu:
Sunana Fatima Abdurrahman Abdu da wace aka fi sani da Teemah ‘Dimple’. Hakika a bangarena, tabbas ina cikin damuwa matuka da gaske akan yadda makarantun boko suka kassance a rufe, hakika hakan ya haifar mun da nakasu a cikin rayuwata gaba daya, kassancewar hakan ya jawo mun koma bayan karatu na sosai, don idan ba dan rufe makarantu da aka yi ba, da yanzu haka na kai wani gaci a gurbin karatuna, saboda muna gaf da fara jarabawa, hakan wannan lamarin rufe makarantu ya faru.
Hakika hakan ya sa na ji rashin dadi sosai, uwa uba ma gashi sakamakon daina karatun ya sa duk irin tanadin da na yi wa jarabawa ta, a baya, yanzu ya zama tarihi, don kuwa duk tanadin da himma da na yi duk sun zube, bana iya tuna komai, sakamakon zama babu karatun ya tsawaita, kuma kassancewar Iyaye na basu da karfin da za su dauko mun mai bani kulawa ta mussaman ba game da karatuna, hakan yana ci mun tuwo a kwarya, kuma na tabbata ire-ire na muna da yawa da muke fuskantar barazanar tarwasewar ilimin boko da muka fara samu, saboda dukkanin abin da baya samun bita to fa wannan al’amari wallahi baya karko, dole ne sai ya zama wata rana babu shi.
Don haka nake kira ga masu fada aji, don Allah su taimaka mana musamman ma wadanda ba mu da karfin dauko masu yi mana lesson a gida, don Allah a dube mu a kawo mana karshen wannan zaman da muke fama da shi babu ilimi, domin ilimi shi ne gishirin rayuwa. Allah ka yi mana jagora Allah ka tallafa mana, amin.
Tabbas wasu makarantu sun yi na mijin kokari wajen gabatar da karatu ta online, Kuma alhamdulillah ana karuwa sosai, kuma Ina fatan a ce duk sauran makarantu su yi dogon nazari akan hakan, suma su fara gabatar da irin wannan karatun ta online musamman makarantun yara kanana da zaki ga wasu zaman gidan yana sa mu manta komai na karatun su, musaman a ce za’a ce irin mu da ba za’a iya daukar musu me lesson a gida ba, Amman wannan karatun ta online sosai zai anfanar da dalibai.
To sai dai muce gwamnati ta yi hakan ne saboda rage yaduwar Korona, Amman shawara ta daya ce rufe makarantun Islamiyya bai yi ba, domin duk inda ake karatun Al’kur’ani sanan duk inda za’a tara yara suna addu’a wallahi a cikin mako guda sai an ga canji ba kadan ba, domin Ubangiji ne ya ce idan wani abin tashin hankali ya zo muku ku yi kokarin dawowa gare ni, ba wai ku kara nesanta kanku da ni ba.
Lokacin da aka yi bom a Kano me ya sa duk ba’a yi Lock down ba, Ina cewa a cikin masallaci aka dasa bom da ya tashi da mutane a cikin garin Kano, Hakan bai hana wani satin an dawo Sallah Jumu’a ba, to don me ya sa yanzu da Korona ta zo aka rufe duk wata hanya ta ibada, aka rufe duk inda musulmi zai je ya yi ibada ya roki Allah ya kawo sauki? idan kasan bakin wani baka san na wani ba. Shawarata a nan ita ce, shugabannin mu su duba maganar bude Islamiyya ko don samun rahma daga mahaliccin mu.

Ibrahim Yakub:


Asalin sunana dai shi ne Ibrahim Yakub, amma sai dai a social media mutane sun san ni ne da Ebraheem Aleeyou Bros (Ebraheem Bros) kasancewar da hakan nake amfani. Ni haifaffen garin Kontagora ne Jihar Neja. Na yi Firamare na a Kontagora Zango Primary School Kontagora, daga nan na dawo Minna inda na fara Secondry school dina a Father O’conel Secondry School Minna a takaice dai yanzu haka Alhamdulillahi ina karatu ne a jami’ar Ahmadu Bello Unibersity Zaria, (ABU ZARIA) ina karanta LAW.
To masha Allah, ni dai zan fadi ra’ayi na ne a matsayi na na dalibi ba Malami ko mai ilimi ba maganar gaskiya rufe makarantu da gwamnati ta yi don gudun yaduwar wannan annobar ba shi ba ne mafita gare mu dalibai ba haka ga duk wani dalibi mai kishin kan shi ya san gaskiya ana so a mayar da mu koma baya dalilin wannan annobar komai zai tabarbare mana ne a fannin ilimi haka da ma lalacewar tarbiyyar wasu yaran.
Abin da ya sa na ce zai iya zama silar lalacewar wasu yaran shi ne yanzu idan kika duba yara kowa yana gida wasu basu sana’ar komai zaune suke kuma akwai miyagun abokai da ba karatun ne a gaban su ba daman abin da ya raba su da su shi ne zuwa makarantar da suke yi to yanzu babu makarantar shi ya sa za su jone sai su dinga bin su wurin harkar daba, kwace, shaye-shaye da sauran abubuwa marasa kyau.
Kamar dai anan minna yanzu haka akwai yara ‘yan kasa da shekaru 18 da suke shiga unguwanni da wukake suna kwacewa mutane kudi waya ko dai wani abun wasun su ma har shaye-shaye suke yi kuma da aka yi duba wadannan yaran duk yawancin su dalibai ne ganin yanzu suna zaman banza ne ya sa suke biyewa yara masu wannan halin kuma suka daukarwa kan su wadannan halayen banzan.
Ya kamata gwamnati ta fahimci halin da ake ciki sanadin rufe makarantu nasan an yi ne saboda gudun yaduwar wannan cutar to fa gwamnati ta sani idan har za ta bari al’umma su koma kasuwanni da wuraren ibadu to za’a iya komawa makarantu domin kamar yadda ake cudanya a makarantu haka ake yi a kasuwanni da wuraren ibadu kamar yadda rayuwa ba ta yiwuwa sai da kasuwanci da ibadu haka kasuwaci da ibada sai da ilimi kuma kowa ya san a makarantu ake koyar da ilimi. Kirana ga gwamnati shi ne ta duba ta bude makarantu amma ta tabbatar da jama’a na bin dokokin kare yaduwar cutar corona da likitoci suka fitar kamar irin sanya face mask wanke hannaye frekuently da sauran su. Gwamnati su yi hadin gwiwa da hukumomin makarantu don tabbatar da an hukunta duk wanda ya karya dokar kare yaduwar cutar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: