An dambata da dama a fafatawar da aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.
Daga cikin wasannin da aka yi har da wanda Aminu Shagon Langa-Langa daga Arewa ya buge Shagon Abata Mai daga Kudu a turmi farko.
Sai dai kuma Bahagon Aleka ne daga Kudu ya fara doke Sani Mai Kifi daga Arewa a turmin farko a wasan da aka fara a safiyar Lahadin.
Damben Autan Horo daga Arewa da Autan Dogon Aleka daga Kudu canjaras aka yi, haka ma wasa tsakanin Usha daga Arewa da Shagon Abata Mai daga Kudu babu wanda ya faɗi.
Sai aka dambata a wasan da Shagon Sama’ila daga Kudu ya yi nasara a kan Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa a turmin farko.
Damben Shagon Fanteka daga Kudu da Shagon Bala Ɗan Zuru daga Arewa babu kisa, haka ma wasa tsakanin Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Ɗan Abata Mai babu kisa.
Wasan daf da ƙarshe da aka dambata kuwa Shagon Nuran Dogon Sani ne daga Arewa ya buge Shagon Autan Faya daga Kudu a turmi na biyu.
Za a ci gaba da wasa ranar lahadi mai zuwa inda da safiyar ranar za a fara fafatawa tsakanin shagon Sama’ila daga kudu da shagon Lawwalin Gusau daga arewa.