Abba Ibrahim Wada" />

Sakamakon Wasan Damben Gargajiya A Abuja

An fafata a wasanni da dama a gidan damben gargajiya a safiyar Lahadi a Dei-Dei da ke a babban birnin tarayya Abuja kuma kamar yadda aka saba kowanne lokaci wasanni sun yi zafi a yayinda maza su ka fadi wasu kuma suka kai bantansu.

Wasannin Da Aka Yi Kisa:

Dan Mutan Karmu ya buge Shagon Dan Jimama

Shagon Bahagon Musan Kaduna ya doke Autan Mai Takwasara

Autan Mai Takwasara ya doke Autan Dan Jimama

Shagon Autan Dan Tagaye ya yi nasara a kan Dogon Na Sigari

Shagon Shagon Dan Bunza ya buge Shagon Sojan Kyallu

Bahagon Audu Argungu ya buge Na Balbali

Dogon Bahagon Sisco ya kashe Autan Dan Bunza

Wasannin Da Babu Kisa:

Bahagon Dan Kanawa da Dan Aliyun Langa-Langa

Garkuwan Autan Faya da Shagon Bahagon Audu Argungu

Shagon Shagon Lawwalin Gusau da Garkuwan Autan Faya

A sati mai zuwa ne kuma za a cigaba da fafatawa a damben inda a ke zaton za a samu manya-manyan ‘yan dambe daga jihohin katsina da Sokkoto da kuma jihar Kebbi wadanda za su samu halartar filin fafatawar saboda a satin da ya gabata ba su samu zuwa ba.

Exit mobile version