Sakataren Gwamnatin Kano Ya Zama Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya tabbatar wa da Sakataren Gwamanatin Jihar Alhaji Usman Alhaji mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sandan sa-kai da aka fi sani da ‘yan sandan sarauniya.

‘Yan sandan sarauniya dai na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro a cikin al’umma, inda suke taya ‘yan sanda da ke aiki karkashin Gwamnatin tarayya.

Nijeriya dai na fuskantar karancin jami’an ‘yan sanda, domin a yanzu yawansu ya zarta dubu 350, inda kusan dubu 80 ke gadin jami’an Gwamnatin kasar nan, wanda hakan ne ya sanya ma’aikatan Gwamnati da kuma nagartattun mutane ke shiga aikin dan sandan sarauniyar domin bayar da gudunmawa.

Tuni dai Majalisar kasa ta bukaci jihohi da su yi dokar da za ta bayar da damar kafa ‘yan sanda na jihohi.

Sai dai kwararru a harkar tsaro na bayyana cewa daukacin tsarin daukar ‘yan sandan ma na bukatar sauyi, ta hanyar kawar da nuna wariya da fifita wasu, in har ana son ganin sauyi mai ma’ana.

An dai tabbatar wa da sakataren gwamnatin karin girman ne a ranar Talatar da ta gabata.

Exit mobile version