Abdullahi Sheme" />

Sakataren Ilimi Na Karamar Hukumar Funtuwa Ya Ziyarci Wasu Makarantu

Sakataren Ilimi

Sakataren ilimi na karamar Hukumar mulki dake Funtuwa a Jihar Katsina Alhaji Sama’ila Ibrahim Abdu ya ziyarci wadansu makarantun Firamare a yankin Karamar Hukumar, sakataren ilimi ya kai ziyarar gani da ido yadda malaman ke zuwa wuraren aikinsu a cikin lokaci da kuma ganin yadda malaman ke maida hankali a wuraren aikinsu, yawan makarantun da Sakataren ilimi ya kai ziyarar gani da ido makarantun Firamaren Aya, Shehu, Idris, Sambo da makarantar B.C.G.A da Shehu inda ya yi ma malaman jawabi su maida hankali wurin koyarwar, su sani amana aka basu kuma Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin Jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari ganin yadda wannan Gwamnatin mai ci a yanzu ta maida hankali wajen bunkasa ilimi musamman ilimin kananan yara watau makarantar firamare ganin yadda aka gyara mafi yawancin dukkan makarantun Firamare na Jihar baki daya musamman na karamar Hukumar mulki da ke Funtuwa.

Alhaji Sama’ila ya kara da cewar babu wata Jiha a Kasar nan da take biyan malaman makaranta albashinsu cikin lokaci da yawan karin girma ga malaman makarantar irin Jihar Katsina ya zama wajibi ku rike aikinku kuma ku hori yaran da su rika zuwa makaranta cikin lokaci kuma idan yara sun yi laifi ba yawan bugu yake sa yara su yi abinda aka ce ba kurari da ba yaro tsoro shi ne ake so.

Sakataren ilimin ya kara gode ma gwamnatin Jihar Katsina tare da dan Majalisar Jihar mai wakiltar Karamar Hukumar a zauren majalisar Alhaji Abubakar Total da kwamishinan ruwa Alhaji Musa Adamu akan yadda suke taimakon karamar hukumar da manya manyan ayyukan da wannan Gwamnatin ta kawo a jihar musamman a Karamar Hukumar Funtuwa.

Alhaji Sama’ila Ibrahim ya yaba ma dukkan makarantun da ya ziyarta inda ya kara yaba ma malaman da kuma iyayen yaran da suke turo yaransu zuwa makarantunsu cikin lokaci, ya kuma nuna gamsuwarshi wajen yadda ake tsaftace makarantun da ya ziyarta, daga karshe ya yi huduba ga dukkan malaman makarantun da yaje da suji tsoron Allah saboda amana ce aka basu kuma ana biyansu hakkinsu kuma idan suka yi algushi wajen aikinsu Allah zai tambayesu gobe kiyama, Sakataren ilimi ya sami rakiyar shugaban ma’aikata na ma’aikatar ilimi ta Karamar Hukumar Alhaji Lawal Aliyu Danmairo, a nashi jawabin daya daga cikin shuwagabannin makarantun firamare ya gode ma Sakataren ilimi na Karamar Hukumar yadda ya yaba ma makarantarshi ta Sambo Firamare, shugaban Makarantar Sambo Malam Hafizu Bala ya kara mika godiyarshi ga Gwamnatin Jihar Katsina tare da Dan Majalisarsu Alhaji Abubakar Total da kwamishinan Ruwa Alhaji Musa Adamu da sauran malaman makarantunshi ta Sambo Firamare yadda suke ba shi goyon baya. A wani cigaba da aka samu Al’ummar kauyen bare bari sun kawoma Sakataren ilimin Alhaji Sama’ila ziyarar godiya a ofishinsa dake Funtuwa yadda yake kokari wajen koyar da yaransu.

 

Exit mobile version