Daga Khalid Idris Doya
Rahotonnin da suke fitowa daga fadar gidan Gwamnatin jihar Bauchi na nuni da cewa Babban Sakataren Lamurran Sirri na Gwamna Bala Mohammed (Principal Private Secretary), Farfesa Mohammed Musa Kirfi ya yi murabus daga wannan mukamin nasa a jiya.
Zuwa yanzu wakilinmu bai jiyo dalilin da ya sabbaba ajiye aikin masa ba.
Sai dai bincike ya nuna cewa ajiye aikin da Farfesa Kirfi ya yi dai shi ne ya kawo adadin mutum hudu masu rike da manyan makaman siyasa da suka ajiye aikinsu bisa dalilai daban-daban a karkashin Gwamnatin PDP ta Gwamnatin Bala Muhammad tun lokacin da ta dare garagar mulki shekaru biyu da suka wuce.
Da yake maida martani kan murabus din PPS din, Kakakin jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya nuna cewa wadanda suka yi murabus din sun kasa sauke nauyin da aka daura musu kamar yadda alamu suka nuna.
Ya ce, duk wani da ya ji ba zai iya tafiyar da ayyukan ofishin da aka ba shi ba, yana da cikakken damar ajiye aikin wanda ta hakan ne gwamna zai samu damar nada wasu da suka fi cancanta kan kujerar domin tabbatar da cigaban jihar da kyautata shugabanci.
Cikakken labarin na tafe.