Sakatariyar Karamar Hukumar Da Ake Wata Guda Ba A Shige Ta Ba A Kano

Sakatariyar

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Kananan Hukumomi ne ke zaman gimshikai guda da al’umma ke samun kusanci da shugabannin da suka zaba, musamman a tsarin demokaradiyya. Hakan ta sanya aka samar da irin wadannan kananan hukumomin har guda 44 a Jihar Kano, wadanda suke da mazabu daga goma zuwa sama, baya ga shugaban da ake zaba, domin jagorantar al’ummar Karamar Hukumar da sauran jami’an Gwamnatin da alhakin gudanar da harkokin mulki ya rataya a wuyansu

Kowacce karamar Hukuma ana kyautata zaton tana da hanyoyin samun kudaden shiga, baya ga kason da doka ta warewa kowacce karamar Hukuma daga lalitar Gwamnatin Tarayya, duk da dai gwamnoni sun zartar da wani tsari wanda daga cikin kason da ya dace a ba su, ladan gabe kawai ake tsakurawa wadannan kananan Hukumomi.

Kila hakan ta sanya aka durkusar da wasu kananan hukumomin bakidaya, wanda hakan ya sa LEADERSHIP A YAU ta fara sanya tabaran hangen nesa, domin kawowa mai karatu wasu daga cikin kananan hukumomin da ba su san da wani romon dimukaradiyya ba, balle kuma a samar masu da wasu ayyukan raya kasa.

Saboda irin wannan halin da kananan hukumomin suka tsinci kansu a cikinsa, idan ka kalli wasu kananan hukumomin sai ka zubar da hawaye, saboda tausayi, musamman rashin kowane irin nau’in cigaba da ake fatan samar wa al’ummar yankin.

Guda daga cikin ire-iren wadannan kananan hukumomi na can arewacin Jihar Kano, wadda aka yi ittafakin ta fi sauran shiga halin tsaka-mai-wuya, domin dai ita ma kamar sauran ana zabar shugaba da kansiloli da duk wani tsari da dimukaradiyya ta tanada, domin kusantar da gwamnati ga jama’a, amma babban abin takaicin shine sakatariyar waccan Karamar Hukumar kamar yadda Wakilin LEADERSHIP A YAU ya gane wa idonsa, ana shafe wata guda ba a shiga cikinta ba, domin gudanar da wani aikin al’umma.

Kama daga shugaban karamar hukumar, kansiloli, mashawarta manyan jami’an gwamnati da aka hakikance yana daga cikin abinda suka yi rantsuwar kama aiki akansa har da halartar wuraren aikinsu kowacce, amma ba wanda ke iya zuwa sakatariyar, domin gudanar da aikin da aka damka amanarsa a wuyansa, kuma ba wanda ma ke iya kwana a Karamar Hukumar, sakamakon rashin kowane irin cigaba da rashin kayan more rayuwa da ake sa ran shugabannin za su samar wa al’umma.

Sakatariyar Karamar Hukumar ita kanta sai dai masu gadi kadai ake iya gani, wanda su ma sun tsara kansu, wasu su zo lokaci kaza da kaza, sakatariyar ta zama wurin kiwon shanu da macizai. Wannan ta sa ba wanda ke sha’awar akai shi wannan Karamar Hukuma da sunan aiki.

Daga cikin muhimman wurare da kowacce Karamar Hukuma ke Alfahari da su akwai kotun da ake gudanar da harkokinsa shari’a, amma idan ka leka cikin wannan kotu ba wanda zai yi zaton mutune na iya zama, lamarin ba kyan gani. Wuri daya ne a fadin Shelkwatar Karamar Hukumar ake iyan hangen motsin al’umma, shi ne Islamic center, idan ka cire ta sai ka rantse da Allah wani kungurmin kauye ka ke, ba shelkwatar Karamar Hukuma ba.

Za mu cigaba daga nan bayan mun kammala tuntubar masu ruwa da tsaki na karamar hukumar, don kawo muku cikakken sunanta, wanda ya yi kamanceceniya da halin da take ciki, da sauran bayanan da suka kamata.

Exit mobile version