Umar A Hunkuyi" />

Sakatarorin Ilimi Na kungiyar NASFAT Sun Yi Taro Domin Samar Da Kudade

Sakatarorin kwamitin ilimi daga dukkanin sassan kungiyar mata Musulmi ta, Nasru-il Lahi-l-Fathi, (NASFAT), sun gudanar da wani taro domin su tattauna hanyoyin da za su bi domin samar da kudin da za su gina Jami’ar Fountain Unibersity, a garin Osogbo.

A wajen taron na su, sun kuma nemi gwamnatin tarayya da ta shigar da manyan cibiyoyin ilimi masu zaman kansu a cikin tsarin tallafin nan ta Tertiary Education Trust Fund (TETFUND).
Sun yi wannan kiran ne a wajen taron nasu na kwanaki biyu na ‘ya’yan kungiyar ta NASFAT, wanda aka yi a harabar Jami’ar ta Fountain Unibersity, da ke Osogbo, a shekaranjiya.
A lokacin tattaunawar na su tare da masu ruwa da tsaki, Mataimakin Shugaban Jami’ar Al-Hikmah Unibersity, Farfesa Ibrahim Taofeek, ya nusar da su cewa, ba fa a kafa Jami’a domin neman riba.
Taofeek, daga nan sai ya yaba wa Shugaban Jami’ar ta Fountain Unibersity, a bisa kyakkyawan shugabancinsa, sannan ya bukace shi da ya ci gaba da kiyaye kyakkyawan tsarin da Jami’ar ke da shi.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Jami’ar ta Fountain Unibersity, Farfesa Sanni, a cikin jawabinsa na maraba, ya bayyana cewa dalilin taron shi ne a samar da kyakkyawan tsari da yanayin tafiyar da Jami’ar.

Exit mobile version