Sake Bude Iyaka: Matsalar Da Manoman Arewacin Nijeriya Za Su Fuskanta
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sake Bude Iyaka: Matsalar Da Manoman Arewacin Nijeriya Za Su Fuskanta

byAbubakar Abba
2 years ago
Iyaka

A shekarar 2019 ne, Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin garkame daukacin iyakokin Nijeriya.

Tsohuwar gwamnatin, ta kuma bayar da umarnin haramta shigo da wasu kaya cikin wannan kasa da kuma fitar da su daga cikin kasar, musamman kayan abinci domin a kara habaka harkokin noma  a Nijeriya tare da samar da wadataccen abinci a fadin kasa baki-daya.

  • Matar Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar Da Bada Tallafin N50,000 Ga Mata Dubu 4 A Gusau
  • Hadarin Da Ya Auku Ya Bankado Karyar Japan Game Da Ruwan Dagwalon Nukiliyar Da Take Zubarwa A Teku

Barin iyakokin kasar kara zube, shi ne ya jawo tabarwarewar tattalin arzikin Nijeriya shekaru da dama da suka gabata.

Haka zalika, kayan da ake sarrafawa a kasar waje ake shigowa da su cikin Nijeriya, su ne suka tilasata wa masana’antu da dama na cikin gida garkamewa.

Wannan ne ya yi sanadiyyar dubban ma’aikatan da suke aiki a wadannan masana’antu rasa ayyukansu.

Ko shakka babu, wannan al’amari a bayyane yake; musamman idan aka yi la’akari da yadda Arewacin wannan kasa ta yi fice wajen habaka fannin tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ta hanyar aikin noma a Nijeriya.

Har ila yau, karkame iyakokin kasar ya samar da damar samun kara bude masana’antun sarrafa shikafa a Arewacin wannan kasa, wanda hakan ya bayar da damar samun dimbin ayyukan yi a yankin.

Haka zalika, rufe iyakokin ya bai wa ‘Yan Nijeriya da dama rungumar wannan fanni na aikin noma, wanda ya yi sanadiyyar karin samar da wadataccen abinci a daukacin fadin kasar.

Misali, daga watan Junairu zuwa na Maris din shekarar 2021, fannin aikin noma ya bayar da gagarumar gudunmawa ga tattalin arzikin Nijeriya, wanda ya kai har kashi 22.35 cikin dari na jumullar tattalin arzikin Nijeriya.

“Rufe iyakokin ya bai wa ‘yan Nijeriya da dama damar rungumar fannin aikin noma, wanda hakan ya sa aka kara samar da wadataccen abinci a daukacin fadin wannan kasa baki-daya.”

Sai dai, wasu ‘Yan Nijeriya da dama, na cike da farin ciki a kan umarnin da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar na sake bude iyakokin Nijeriyan, musamman domin ci gaba da shigo da shinkafa, tumatir da kuma sauran kayayyaki zuwa cikin gida Nijeriya.

Har wa yau, a bangaren manoma musamman wadanda ke Arewacin Nijeriya, wannan umarni na Tinubu zai iya jefa makomar rayuwarsu cikin wani mawuyacin hali.

Kazalika, akasarin mazauna yankin na Arewa wadanda suka dauki sana’ar aikin noma, damina da rani das hi suka dogara.

Sannan, bude iyakokin kasar zai iya kassara kayan da ake sarrafawa a Arewacnin Kasar, wanda akasarin masana’antun ba za su iya yin gasa da kayan da ake  sarrafawa a  kasashen ketare ba, wanda hakan kuma kai tsaye zai karya farashin kayan amfanin gona na manoman da ke wannan yanki.

“Bugu da kari, sake bude iyakokin wannan kasa, zai  kawo wa kayan da ake sarrafa wa a Arewa babban nakasu, musamman ganin cewa, mafi yawancin masana’antun ba za su iya yin gasa da irin kayan da ake sarrafawa a kasashen ketare ba, wanda hakan kuma zai karya farashin kayan amfanin gonan manoman da ke wannan yanki.”

Sai dai, wasu mutane da ke yankin na Arewa ba sa yin la’akari da yadda ake yakar hare-haren ‘yan bindiga ta kowanne bangare, misali’ tun daga fannin ilimin boko, aikin noma da sauran harkokin kasuwanci.

Don haka, yanzu lokaci ya yi da gwamnatin tarayya ta hanyar Babban Bankin Nijeriya (CBN), za ta sake auna fa’ida da kuma rashin fa’idar sake bude iyakon kasar tare da daukar matakin da zai fi zama mai sauki ga ‘yan Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Amfanin Kankana Ga Lafiyar Jiki Da Ta Iyali 

Amfanin Kankana Ga Lafiyar Jiki Da Ta Iyali 

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version