Abubakar Abba" />

Sake Fasalin Hukumar Kwastam Babban Aiki Ne – Ali

Kwantirolan Janar na Hukumar hana fasakwauri ta kasa Kanal Hameed Ali mai murabus ya bayyana cewar tsare-tsaren do aka samar a hukumar suna da kalubale amma za’a iya cin nasara.

Ali ya bayyana hakan ne a jawabin sa a lokacin yaye dalibai arba’in na kwalegin ma’aikatan hukumar a garin Abuja, inda ya kara da cewa daga cikin nauyi uku da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dora masa don sake sarrafa hukumar da samar da tsari da kuma tarawa gwamnati haraji ayyukan suna tattare da kalubale.

Yaci gaba da cewa, kasar ta fara cin moriyar wasu tsare-tsaren da aka kaddamar dasu sai dai har yanzu akwai wasu jami’an hukumar da basu rungumi tsare-tsaren ba.

Da ya juwa ga wadanda aka yayen ya shawarce su dasu yi amfani da horon da suka samu a kwalejin don zamowa jakadun chanji na hukumar a dukkan fannonin ta, ya kara da cewa ayau mun samu nasarar kai hukumar zuwa matsayi babba domin kuwa mutane suna girmama jami’anta da kuma fara samar da chanji a hukumar akan yadda take gudanar da ayyukanta..

Acewar sa,“ bama tambayar a bamu cin hanci amma sai dai, wasu na ci gaba da yi amma ba a wurare da dama ba.

Daga cikin arba’in da aka yaye, tara mata ne .

A jawabin sa tunda farko, Kwamandan na Kwalejin Eporwei Edike yace,Kwalejin zata ci gaba da yaye dalibai da zasu samar da chanji akan tsare-tsaren da hukumar take kanyi.

Exit mobile version