Sake Fasalin Kasa: Buhari Ya Jaddada Aniyarsa Na Bin Bukatun ‘Yan Nijeriya

Kasa

Daga Mahdi M. Muhammad,

A jiya Alhamis ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, majalisar kasa wacce alhakinta ke kan tabbatar da cewa kundin tsarin mulki ta amsa kira ga sake fasalin Nijeriya, tuni ta kammala shawarwarin yanki.

Shugaban ya yi wannan yabo ne yayin da yake karbar bakuncin INC na kasa karkashin jagorancin Farfesa Benjamin Okaba.

‘’Da zaran sun kammala aikin, matakin da ya kamata ba zai jinkirta daga bangare na ba,” in ji shi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya yaba wa shugabancin kungiyar ‘Ijaw National Congress’ (INC) kan tabbatarwar da suka yi na hadin kan Nijeriya da kuma tallafa wa yaki da rashin tsaro ta hanyar kirkiro hanyoyin shawo kan lamarin.

Ya roki shugabannin kungiyar da su yi amfani da tasirinta wajen tabbatar da cewa mun ci gaba da aiki tare don ci gaba da kasancewar kasar nan dunkulalliya, ba za ta rarrabu ba, ta yadda za mu iya magance matsalolinmu tare kuma mu shawo kan kalubalenmu tare.

Shugaban kasar ya kuma yi amfani da wannan dama wajen magance wasu bukatun kungiyar a kan batutuwa da dama da suka hada da lalata muhalli, sake fasaltawa, kirkirar jihohi, rabon lasisin aiki ga yankunan Ijaw, kaddamar da Kwamitin hukumar kula da ci gaban Neja Delta (NDDC), da sauransu.

Dangane da bayar da lasisin gudanar da aiki ga yankin Ijaw ga ‘yan kabilar Ijaw, Shugaban kasar ya ce, “yayin da ya amince da bukatar gaba daya, tsarin bayar da lasisin yana karkashin ka’idoji ne wadanda galibinsu sun fi son abubuwan cikin gida da ‘yan kwangila na cikin gida. Ban ga dalilin da zai hana a ba su irin wannan lasisin ba idan sun cancanta.’’

A kan NDDC, Shugaban ya yi alkawarin cewa za a waddamar da kwamitin da zaran an gabatar da rahoton kididdigar binciken kudi.

Ya ce, ‘’Batun da ke jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan kabilar Ijaw na baya-bayan nan shi ne bukatar da hukumar raya yankin Neja Delta ta yi na biyan kudaden ta hanyar isar da taimakon da ake bukata ga mutanen yankin.”

“Dangane da rashin kyakkyawan shugabanci wanda a baya ya sha gaban NDDC, aka kafa binciken kwakwaf kuma ana sa ran samun sakamako a karshen watan Yulin, 2021,” in ji shi.

A jawabinsa, Farfesa Okaba ya bukaci Shugaban kasa ya umarci ma’aikatar albarkatun man fetur da ta ba da umarnin sauya hedikwatar dukkan kamfanonin mai zuwa wuraren ayyukansu na aiki a cikin Ijaw da yankin Neja Delta.

“Dalilin rashin tsaro ya zama abin dogaro ne don sanin kowa ne cewa babu inda a Nijeriya ya fi wani aminci. Abu na biyu, sake fasalin manyan tashoshin jiragen ruwa a Onne, Warri, Port Harcourt, Bonny zai hanzarta ci gaban tattalin arziki, rage rashin aikin yi, aikata miyagun laifuka na matasa da kuma ba da gudummawa ga hadin kan kasa da kwanciyar hankali,” in ji shi.

Da yake sake tabbatar da cikakken tabbaci a kan gaba daya da kuma amfanin juna na tarayya ta gaskiya da kuma kula da albarkatu zuwa ga ci gaba da kwanciyar hankali a Nijeriya, Okaba ya tabbatar wa Shugaban kasar cewa Ijaws ba su da wata manufa ta ballewa ba.

Exit mobile version