Sake Fasalin Tsarin Shari’a Ne Zai Rage Cunkoso A Gidajen Yari – Barista Aminu Bello

Barista Aminu Bello Salihi shi ne baban Jami’i mai kula da ɗaukaka ƙara na kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano, kuma Sakatere a Kwamitin Rage Cunkoso a gidajen yarin Kano. A wannan tattaunawa da Mustapha Ibrahim Tela, Barista ya bayyana aikin kwamitin da irin matsalolin da ke kawo cunkoso a gidajen yari da abun da ke kawo jinkirin Shari’a a gaban Alƙalai a kotuna. Ga yadda ta kaya.

Barista, menene aikin wannan kwamiti da kuke ciki?

Aikin wannan kwamiti shi ne ne ya zagaya ko ina a gidajan yarin da ke Kano domin ganin an ɓullo da hanyoyin da za a rage cunkoso. Har ila yau, kamar yadda aka sani ni ne sakatare a wannan kwamiti da babban mai shari’a na jihar Kano ya kafa.

Baya ga zagayawa gidajen yari, har ila yau, kwamiti yana zagaya kotunan Jihar domin ya duba shara’o’i ta hanyar bincika wa ya gani, idan shari’a ta daɗe mai ya kawo daɗewarta, sannan kuma a ɗauki mataki don ganin komai yana tafiya daidai da doka.

 

Ana fama da cunkuso a gidajen yarin, sau tari za ka ga wurin da aka gina don mutum 500 sai ka ga mutane 1500, me kake ganin yake janyo haka?

To gaskiya alal haƙiƙa cunkoso a gidajen maza wato kurkuku ba al’amari ne na mutum ɗaya ba. Idan ka yi maganar yanke hukuncin aikata miyagun laifuka a Nijeriya bai shafi mutum ɗaya ko hukuma ɗaya ba. Abu ne da ya haɗa hukumomi da yawa ba maaikatar shari’a kaɗai ba. Misali akwai maganar ‘yan sanda, ma’aikatar gidan yari, ma’aikatar shari’a, lauyoyi da sauransu duk suna cikin waɗanda ka iya kawo cunkoso a gidajen yari.

Haka kuma akwai buƙatar a san wani abu shi ne, akwai dokoki a tsare da aka shirya a tsarin shari’ar Nijeriya ga su kansu alƙalai, kotuna, gidajen yari waɗanda suka a matsayin rigafi ka wannan cunkoso, amma wani lokaci matsalar tana taso wa ne daga waɗanda na lissafo a baya, kuma kowa abun yana damunsa ƙwarai da gaske. A lokaci babban mai shari’a na ƙasa da ke Abuja ya ziyarci gidajen yari domin rage cunkoson, an yi abun da ya kamata na ragewar kuma mu ma nan ana yin duk wani ƙoƙari na ragewa.

Kwananan Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ɗauki matakai na ganin an rage cunkoso, inda mu muka je muka yi aikin bisa umarnin gwamna, aka sallami sama da mutane 500, aka kuma ciki duk wata ƙa’ida ta sakin waɗanda aka yi wa afuwa. Kuma duk abinda doka ta bawa Gwamna dama aka yi aiki da ita kuma aka sa ke su. Kuma mutane suna bata gudunmawarsu a ɗai-ɗaikunsu kuma ana samun raguwar cunkoson.

 

Ta yaya kake ganin za a shawo kan wannan matsala?

To gaskiya wannan matsala ce babba kuma ta dami kowa, don haka yadda za a gyara ta shi ne sai an gyara tsarin shari’ar tun daga tushe. Duk wani abu da ya ke kawo cikas an kawar da shi, domin tsarin yana buƙatar gyararraki kamar yadda wasu Jihohin suka fara to ana buƙatar ya game ƙasar. Babbar matsalar mutum ya zauna shekara da shekaru wani ma har ya cinye lokacin da ya kamata ya yi amma ba a yi shari’a ba, wannan babar damuwa ce kuma ya ka mata a kawar da ita a ko ina.

 

Menene makomar mutumin da ya shekara biyar yana sauraron hukunci kuma idan an yake hukuncin ya cinye sama da shekarun da zai yi?

Dama ai abun da ba a so kenan ya faru, shi isa ake da buƙatar a yanke shari’a daga zarar ta zo. Ko da yake ba a ko wane laifi ne ake samun irin wannan matsala da kake magana ba. Yawanci an fi samu a manyan laifuka kamar fyaɗe, sata, kisan kai, zamba cikin aminci, cin amana da dai sauran manya-mayan lafuffuka.

 

Shin akwai dangantaka tsakanin kwamitinka da ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama?

A tsarin kwamitinmu dai muna da dangantaka mai kyau da irin waɗannan ƙungiyoyi da ka ambata. Muna da kyakyawar fahimta sosai mai kyau da ƙungiyar lauyoyi musulmi ta jihar Kano kuma sun nuna sha’awarsu za su shigo a wannan aiki na alheri. Kuma akwai ƙungiyar taimako ta lauyoyin (Legal Aid Council) duk muna tare da su a wannan aiki.

 

Da kafa wannan kwamiti naku, wacce nasara kake ganin an samu?

Shakka babu duk wanda ya je gidajen yarin Kano zai ga ayyukan da wannan kwamitin ya yi da kafa shi zuwa yau, wanda zan iya bugar ƙirji in ce an samu nasara.

Duk da cewa ana samu ƙalubale ta fuskar shari’a, amma mu a kotunan Musulunci ana samun ci gaba ƙwarai. Ina tabbatar maka ko a wannan lokaci da Gwamna ya biyawa wasu diyya aka sake su, cikin sama da 200 da aka bamu za ka ga cewa na ɓangaran kotunan musulunci da aka saki ba su fi kimanin 50 ba, sauran duk daga sauran kotuna suke. Kasancewar muna bin matakai kala-kala don ganin a sasanta wasu abubuwan.

Kuma wannan kwamiti na wayar kan alƙalai cewa, duk wata hanya da doka ta yadda da ita ta sulhu a bi ta, in dai maganar kuɗi ne ko wani abu, a sulhun ta domin ɗaurin ba shi ne mafita ba. Haka kuma su kansu gidanjen yari suna ba mu haɗin kai, duk sanda wannan kwamiti ya ziyarci gidan yari ko ranar aiki ko ba ranar aiki ba suna ba mu haɗin kai na mu ga mun gana da ɗauraru na gidan yari komai yawansu, domin mu ji bayanansu duk dai a mataki na rage cunkoso to wannan babbar nasara ce.

 

Me kake ganin yake kawo jinkirin shari’a a gaban alƙalai?

To kamar yadda ka sani, ita shari’a lamari ne mai haɗarin gaske, domin shi alƙali yana aiki ne da abun da aka gaya masa na zahiri tun da shi bai san gaibu ba. To kuma a baya na gaya maka cewa dalilai masu yawa ne ya ke kawo cunkoso a gidajen yari, to haka ita ma shari’ar irin waɗannan ne suka kawo a daɗe ba a ga ma ba. Wani lokaci an kusa kammala shari’a ko a na tsaka da yinta sai lauyoyi su rubuto takarda su na buƙatar a tsaida ita ko wani abu mai kama da haka to duk waɗannan suna kawo jinkiri a daɗe ba a gama shari’a ba, da dai sauran abubuwa irin waɗannan.

 

A ƙarshe, wane saƙo kake da shi?

Saƙona na ƙarshe shi ne, mutane su guji mummnan zargi akan abun da ba su sani ba kamar yadda addininmu ya tanada. Kuma ina so mutane duk wadda zai kai ƙara kotu to ya nemi waɗanda su ka san abun idan ba shi da lauyoyi. Ba shakka kotuna na taka rawa sosai wajen kawo zaman lafiya a cikin al’umma saboda haka yana da kyau mutane kowa ya tsaya a matsayin sa na mutum mai son zaman lafiya da bin dokoki kamar yadda ya kamata, kuma duk masu ruwa da tsaki a shari’a da sauran fannonin rayuwa a sanya tsoron Allah a zukata.

Exit mobile version