Daga Muhammad Maitela,
A fadi-tashin lalabo hanyoyin da za su taimaka wajen sake farfado da jihar Borno, a ranar Alhamis Gwamna Umara Zulum ya gana da sabuwar wakiliyar Tarayyar Turai a Nijeriya, Misis Cecile Tassin-Pelzer a Abuja.
A lokacin wannan ziyara a ofishin ta (EU House), Gwamna Zulum ya bukaci kungiyar Tarayyar Turai ta dauki matakan aiwatar da ingantattun kudurorin raya yankunan karkara a jihar Borno.
Har wala yau, Gwamnan ya gabatar wa da wakiliyar Tarayyar Turan bukatar neman karin gudanar da ayyukan ci gaban jihar, tare da yaba mata dangane da ci gaba da goyon bayan da ta ke bai wa jihar.
Haka kuma, Zulum ya ankarar da EU wajen sanya ido a gudanar da wasu muhimman ayyukan ci gaba na hadin gwiwa da kungiyoyin bayar da agaji ke aiwatarwa a jihar. Haka kuma ya taya babban jami’in murnar kasancewa wakili a Nijeriya tare da bashi tabbacin samun goyon baya.
“Wanda tun a lokacin da nake kwamishina, ina da kyakkyawar alaka tsakanina da Tarayyar Turai, kuma makasudin zuwa na shi ne taya ka murna zuwa Nijeriya.”
A nata jawabi, Misis Tassin-Pelzer ta bai wa Zulum tabbacin ci gaba da samun hadin kai da kyakkyawar alaka tsakanisu da gwamnatin jihar Borno.
Ta kuma kara bai wa Gwamna Zulum tabbacin cewa ta hanyar tarayyar Nijeriya za su ci gaba da bayar da fifiko wajen talkafa wa yan gudun hijira da aiwatar da shirye-shiryen ci gaban kasa.
Kafin nada ta wakiliya a Nijeriya, Misis Tassin-Pelzer ita ce wakiliyar Tarayyar Turai a kasar Senegal tsawon shekaru uku.