A jiya ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gargadi gwamnatin tarayya a kan sake kakaba dokar takaita zirga-zirga a cikin kasar nan, ya bayyana cewa saka dokar zai yi matukar raunata tattalin arziki wanda hakan babban matsifa ce ga ‘yan Nijeriya. Wannan yana cikin kalamun gwamnan CBN, Godwin Emefiele wanda ya bayyana jim kadan bayan fitowa daga farkon toron kwamitin tsare-tsaren kudade wanda ya gudana a jiya a garin Abuja.
Emefiele ya ce, “kamar yadda ake ta kokarin samo magungunan rigakafin cutar Korona domin samun lafiya mai daurewa, kwamitin tsare-tsare ya bukaci gwamnati a kan kar ta kuskura ta kakaba dokar takaita zirga-zirga domin zai yi matukar raunata tattalin arzikin Nijeriya, wanda hakan zai hana a samu wani riba kamar yadda ba a damu ba a shekarar 2020.”
“Dalilin da ya sa muke bayar da shawara kar a sa dokar hana zirga-zirga karo na biyu a Nijeriya shi ne, saboda babban mutsiba ce ga kowani dan Nijeriya da kuma tattalin arziki, mun kwashe watanni 12 muna samun kashi biyar na kudaden ruwa da CBN ke bayarwa.
“Hakan ba karamin asara ba ce a gare mu musamman ma a dai-dai lokacin da muke kokarin farfadowa, amma za mu yi kokari bin wasu hanyoyi ta yadda CBN za ta kara fadada asusunta ga wasu bangarori na musamman kamar irin su kananan kasuwanci da harkokin lafiya da bangarin noma, wanda za mu ba su goyan bayan kara sana’antarwarsu , domin samun ci gaban wannan kasa.
“Saka dokar hana zirga-zirgab zai durkusar da ayyukan tattalin arziki da kawo matsaloli a cikin rarraba kayayyaki da shafar samar da kayayyaki wanda a yanzu haka yake bukatar tsayuwa da kafarsa da samun damar faefadowa a cikin ‘yan kankanin lokaci.
“Kwamitin za ta bibiyi tsarin harkokin kudade na dukkan cibiyoyin harkokin kudade domin rage farashin basussuka da bambamta kudin ruwa na bashi da samar da mahimman ka’idojin biyan bashi.
“Haka kuma kwamitin zai sake bibiyan yadda ake samun hauhawar farashin kayayyaki tare da samar da tsarin magance matsalar wajen bunkasa bayar da basuka ga magidanta da kananan kasuwanci da harkokin noma da dai sauran su wanda hankan zai samar da ayyukan yi da kuma kara bunkasa tattalin arziki a cikin kasar nan.
“Domin haka, kwamitin zai sake bibiyan sha’anin kudade tare da samar da tsare-tsaren harkokin bunkasa kudade, domin magance matsalolin tattalin arziki ga ‘yan Nijeriya wacce korona ta haddasa,” in ji shi.
Emefiele ya bayyana cewa, Babban Bankin Nijeriya ya zuba tsafar kudade wanda suka kai naira tiriliyan biyu a cikin tattalin arziki a hanyar mabambamtan bayar da tallafin kudade.
Ya ce, “domin farfado da harkokin kudade daga matsalolin cutar Korona, bankin ya yi kokarin zuba kudade masu matukar yawa a shekarar 2021. Inda a wannan watan Junairun shekarar 2021, bankin ya rarraba naira tiriliyan biyu.
“Akwai shirin bayar da tallafin cutar Korona ga magidanta da kananan kasuwanci wanda muka raba naira biliya 192.64 ga matane guda 426,016. Haka kuma mun rarraba naira biliyan 106.96 ga mutane 27,956 a karkashin shirin bayar da tallafi ga kananan noma, yayin da a bangaren lafiya, mun rarraba naira biliyan 72.96 wajen gudanar da ayyuka guda 73 da ayyukan wuraren shan magani guda 26 da asbitoci duda 47 da cibiyoyin kula da lafiya a cikin kasar nan.
“CBN ya rarraba wa wadanda suke bukata kudade wadanda suka kai na naira biliyan 194.6, domin zuba jari na lokaci mai tsawo a bangaren harkokin kudade saboda bunkasa ababen more rayuwa da wajen farfado da tattalin arziki domin samun nasarar ci gaba mai daurewa. Daga karshen watan Satumbar shekarar 2020, an kashe jimillar kudade na naira biliyan 166.2 ga ayyuka guda 25 a karkashin wannan shirin.
“Bankin ya rarraba wa manoma guda 10,105 kudade na naira biliyan 1.0 a watan Satumbar shekarar 2020. Wadannan kudade sun karu da kashi 221.8 fiye da na watan Agustar shekarar 2020. Bincike ya nuna cewa, jihohi 28 cikin har da Abuja suka ci gagarumar moriyar shirin na kudade na naira miliyan 404.2, yayin da jihohin da suka sami karancin cin moriyar shirin sun hada da Adamawa da kuma Sakkwato wanda suka sami naira miliyan 0.8.
“A bangaren noman kasuwanci kuma, bankin ya rarraba naira biliyan 26.99 ga mutanen da suka ci moriyar shirin guda 6,372 a watan Satumbar shekarar 2020, wanda idan ana hada da na karshe watan Satumbar shekarar 2020 an rarraba jimillar kudade wanda suka kai na naira biliyan 66.2 ga mutanen da suka ci moriyar shirin guda 17,541.
“Domin samar da damarmakin ayyukan yi ga matasan Nijeriya kuwa, CBN ya samar da kudade ga shirin hororar da matasan Nijeriya kudade na naira biliyan 3.12 ga wadanda suka ci moriyar shirin guda 320 da kuma naira miliyan 268 ga mutane 395.”
Emefiele ya kara da cewa, Babban Bankin Nijeriya ya saka ranar 31 ga watan Junairu ga masu fitar da kayayyaki da su yi kokarin cika ka’idojin fitar da kayayyaki daga Nijeriya.